Hari a Chakawa da Kawu
Iri | Kisan Kiyashi |
---|---|
Kwanan watan | ga Janairu, 2014 |
Ƙasa | Najeriya |
Adadin waɗanda suka rasu | 138 |
Hare-haren Arewacin Najeriya a watan Janairun 2014 wani jerin kisan kiyashi ne na ƴan ta’adda da suka faru a watan Janairun shekara ta dubu biyu da goma Sha hudu 2014 a Kawuri, Jihar Borno da kuma a kauyen Chakawa, karamar Hukumar Madagali, Jihar Adamawa (hari a lokaci ɗaya, amman wuri daban-daban). An dai ɗora alhakin dukkan hare-haren kan ƴan kungiyar Boko Haram wacce tayi ƙaurin suna wajen kai hare-hare, musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A ranar 31 ga watan Janairu, an kashe wani fasto da membobin ikilisiyarsa su 10 a Chakawa. [1] [2]
26 ga watan Janairu
[gyara sashe | gyara masomin]A daren ranar ashirin da shida 26 ga watan Janairu an kai wasu hare-hare guda biyu a Kawuri, jihar Borno da cocin Katolika ta ƙauyen Chakawa, karamar hukumar Madagali, jihar Adamawa . [3] [4] [5]
A Kawuri, wani ƙauye a karamar hukumar Konduga, jihar Borno (wanda ke da tazarar kilomita 37 daga kudu maso gabashin Maiduguri ), an kashe mutane 85 cikin dare. [6] [7] [8] Ana dai ɗora alhakin hare-haren kan kungiyar Boko Haram . [9]
A Chakawa (garin da aka fi sani da sunan Waga Chakawa) an yanka maƙogwaron wasu da yawa daga cikin masu bauta a cocin,[10] yayin da aka harbe wasu. An kiyasta cewa an kashe mutane 31, [11] amma adadin ya ƙari zuwa 41. [12]
Adadin waɗanda suka mutu na karshe ya kai a ƙalla jummullar mutane 138. [13]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Gunmen invade church, kill pastor, 10 worshippers in Adamawa. Samuel Agada, Daily Post Nigeria. February 2, 2014.
- ↑ Kill Pastor, 10 worshippers In Adamawa. February 2, 2014 - 5:31am | Lara Adejoro, Daily Times of Nigeria.
- ↑ BBC world news, 27 January 2014.Nigeria 'Boko Haram' attacks leave scores dead.
- ↑ Communal unrest turns deadly in Nigeria. AlJazeera English website. Accessed 25 May 2014.
- ↑ Gunmen kill worshippers at Nigeria church. AlJazeera English website. Accessed 25 May 2014.
- ↑ HARUNA UMAR. 85 dead in Nigerian village massacre. January 28, 2014 at 09:14pm.
- ↑ Boko haram: 85 dead and counting in northeast Nigeria village Archived 2014-05-29 at the Wayback Machine, Wednesday, 29 January 2014 12:36.
- ↑ Reuters News Agency.Death toll in northeast Nigeria attack rises to 85 Archived 2020-07-28 at the Wayback Machine, Tue Jan 28, 2014.
- ↑ Ibrahim-Gwamna Mshelizza. Not Less Than 50 Killed In Kawuri Today. The Nigerian Voice. 27 January 2014.
- ↑ "How Boko Haram Slit Throats Of Church Worshippers In Adamawa [GRAPHIC] | 9JAOLOFOFO™". 9jaolofofo.com.ng. Archived from the original on 2014-05-25. Retrieved 2014-05-25.
- ↑ By Saharareporters, New York Jan, 29 2014, 9:01AM. Adamawa Bishop Says Boko Haram Killed 31 Of His Parishioners. Archived 2014-05-25 at the Wayback Machine
- ↑ Sunday, 02 February 2014 05:00. Kabiru R. Anwar, Chakawa death toll rises to 41; pastor killed in fresh Hyambula attack.
- ↑ Ndahi Marama & Umar Yusuf, January 29, 2014. Adamawa church attack: Death toll rises to 138. Vanguard Nigeria.