Hari a Yola, Nuwamba 2015
Appearance
Hari a Yola, Nuwamba 2015 | ||||
---|---|---|---|---|
suicide bombing (en) | ||||
Bayanai | ||||
Kwanan wata | 27 Nuwamba, 2015 | |||
Wuri | ||||
|
A ranar 17 ga watan Nuwamban 2015, An kai harin ƙuna baƙin wake a kasuwar kayan lambu da ke Yola, Jihar Adamawa, a gabashin Najeriya. [1] Sama da mutane 30 ne suka mutu yayin da wasu 80 suka jikkata yayin da ‘yan kasuwa a birnin ke rufewa. [1]
Alhakin kai harin
[gyara sashe | gyara masomin]Ana zargin ƙungiyar Boko Haram mai da’awar jihadi – wanda rikicinta ya faro tun a shekarar 2009 kuma ya kai a tsakiyar shekarun 2010 – ana zargin su ne suka kai wannan hari da wasu da dama a jihar Adamawa. [1] [2] Waɗanda sun haɗa da tashin bam a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Yola a watan Satumbar 2015, [2] [1] da kuma wanda ya faru a Mubi a 2012, 2014, 2017 da 2018.