Jump to content

Harin bam a Najeriya, Fabrairu 2015

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harin bam a Potiskum da Kano
suicide bombing (en) Fassara
Bayanai
Kwanan wata 15 ga Faburairu, 2015, 22 ga Faburairu, 2015 da 24 ga Faburairu, 2015
Wuri
Map
 11°42′33″N 11°04′10″E / 11.7092°N 11.0694°E / 11.7092; 11.0694

A watan Fabrairun 2015, an kai harin ƙuna baƙin wake a garuruwan Damaturu da Potiskum da kuma Kano da ke arewacin Najeriya.[1] [2] [3]

A ranar 15 ga watan Fabrairun 2015, wata budurwa ƴar ƙuna baƙin wake ta tarwatsa kanta da karfe 1:00 na rana a wata tashar mota da ke da cunkoson jama’a a garin Damaturu, jihar Yobe, inda ta kashe akalla mutane 16 tare da raunata wasu 30. [2] Wannan dai shi ne harin ƙuna baƙin wake na farko a Damaturu. [2]

A ranar 22 ga watan Fabrairun 2015, wata yarinya ‘yar ƙuna baƙin wake ta kashe mutane biyar ciki har da ita, tare da raunata wasu da dama a wani shingen binciken jami’an tsaro da ke wajen wata kasuwa a garin Potiskum na jihar Yobe.[1] [3]

Birnin Kano

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 24 ga watan Fabrairun 2015, wani ɗan ƙuna baƙin wake ya tayar da bam a lokacin da yake kokarin shiga motar bas a tashar motar Dan-Borno da ke Potiskum, inda ya kashe mutane 17, sama da 30 suka jikkata tare da lalata motar. [1] Bayan sa'o'i kaɗan a wannan rana, a birnin Kano wasu ƴan ƙuna baƙin wake biyu sun tayar da bam a tashar motar Kano Line, inda suka kashe mutane 10. [1]