Harin bam a Nyanya, Mayu 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHarin bam a Nyanya, Mayu 2014
Map
 9°03′N 7°30′E / 9.05°N 7.5°E / 9.05; 7.5
Iri aukuwa
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 1 Mayu 2014
Wuri New Nyanya
Adadin waɗanda suka rasu 19
Adadin waɗanda suka samu raunuka 80

A ranar 1 ga watan Mayu, 2014, wata mota ɗauke da bam ta fashe a New Nyanya, wani gari a jihar Nasarawa, Najeriya. Fashewar ta yi sanadin kashe aƙalla mutane 19 tare da jikkata wasu su 60.[1]

Wai-wa-ye[gyara sashe | gyara masomin]

Sama da mutane dubu 15,000 ne aka kashe a Najeriya cikin shekaru 15 da suka gabata a mabanbanta rikice-rikice. Yawancin hare-haren na da alaƙa da dalili na addini; kuma hakan ya samo asali ne daga buƙatun shari'ar Muslunci da ta maye gurbin babbar doka ta Tarayyar Najeriya. Ana danganta ƙungiyar Boko Haram da kai hare-haren.[2] waɗannan ayyukan gabaɗaya ba a danganta su ga kowane takamaiman ƙungiya ko shugaba ba.

Kai hari[gyara sashe | gyara masomin]

Wata mota ɗauke da bama-bamai a cikinta ta isa wani shingen bincike na ƴan sanda. Da isar ta dai-dai wurin duba ababen hawa, sai wani mutum ya fito daga cikin motar ya fara gudu yayin da motar ita kuma ta tarwaste sakamakon ababen fashewar da ke cikin motar. Hakan ya sa wasu motocin dake kusa da wajen, suka kama da wuta, suma suka fashe. A cewar Sufeto Janar na ƴan sandan, Frank Mba, jimillar motoci shida ne suka tarwatse sakamakon bam ɗin da aka dasa a cikin motar da aka zo da bama-baman da ita. Harin dai ya faru ne a kusa da yankin da wani bam ya taɓa fashewa a watan da ya gabata.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Abuja blast: Car bomb attack rocks Nigerian capital". BBC News. 2 May 2014. Retrieved 3 May 2014.
  2. "A dangerous new level". The Economist. 3 September 2011.
  3. "Death toll rises from car bomb in Nigerian capital Abuja". The Guardian. 2 May 2014. Retrieved 3 May 2014.

Coordinates: 9°03′00″N 7°30′00″E / 9.0500°N 7.5000°E / 9.0500; 7.5000