Harin bam a Nyanya, Afrilu 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHarin bam a Nyanya, Afrilu 2014

Map
 9°03′N 7°30′E / 9.05°N 7.5°E / 9.05; 7.5
Iri bomb attack (en) Fassara
Kisan Kiyashi
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 14 ga Afirilu, 2014
Wuri New Nyanya
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 75
Adadin waɗanda suka samu raunuka 124

A ranar 14 ga watan Afrilu, 2014 da misalin ƙarfe 6:45 na safe, wasu bama-bamai biyu sun tashi a wata tashar mota mai cunkoson jama’a, a garin Nyanya na Jihar Nasarawa, hakan ya jawo mutuwar mutane aƙalla 88 tare da jikkata wasu 200. Tashar motar na da nisan kilomita 8 ne  daga kudu maso yammacin babban birnin tarayya.[1][2][3][4][5]

Kungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kai harin kwanaki shida bayan faruwar lamarin. Hakan ya faru ne sa'o'i kaɗan kafin a sace ƴan matan Chibok.

Kai hari[gyara sashe | gyara masomin]

Wani mutum yana hutawa a asibiti biyo bayan mutuwar mutane 71 yayin da aƙalla 124 har dashi suka jikkata, sakamakon harin a wata tashar mota da ke wajen birnin Abuja, 15 ga Afrilu, 2014.

Wasu bama-bamai da aka ɓoye a cikin motoci sun tashi da sanyin safiya a wata tashar mota da ke Nyanya a wajen Abuja. Bayan fashewar farko, an sake samun tashin bama-bamai yayin da tankunan mai a cikin motocin da ke kusa da su suka tarwatse.[6]

Abbas Idris, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a Abuja, ya tabbatar da mutuwar mutane 71 tare da jikkata wasu 124.[7] Tashar motar na yi wa talakawa da wasu ƙabilu ko mabiya wani addini, hidima.[4] Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, Manzo Ezekiel, ya tabbatar da cewa da yawan waɗanda suka jikkata na samun kulawa a asibiti.[7] Ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, adadin waɗanda suka mutu ya karu zuwa 75, yayin da masu bincike ke ci gaba da zaƙulo tarkacen da aka samu a wurin da fashewar ta afku.[1] Har wayau ya zuwa ranar 18 ga watan Afrilu, adadin waɗanda suka mutun ya ƙaru zuwa 88, yayin da fiye da 200 aka ruwaito sun jikkata.[5]

Nauyi[gyara sashe | gyara masomin]

Kungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kai harin, kwanaki shida bayan faruwar lamarin—a cikin bidiyon da ya nuna su a lokacin da su ke ɗaukar alhakin kai harin, ya kunshi shugaban kungiyar Abubakar Shekau wanda aka saki a ranar 19 ga watan Afrilu.[8] Hukumar ƴan sandan kasa da kasa ta Interpol ta kama Aminu Sadiq Ogwuche a kasar Sudan a watan Mayun 2014, bisa zargin kasancewar sa a cikin ɗaya daga cikin waɗanda su ka kai harin bam ɗin.[9] Sa'o'i kadan biyo bayan harin, ƴan ƙungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da ɗaruruwan ƴan matan makarantar Chibok.

Martani[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ziyarci wurin da fashewar ta faru, inda ya ce:

Mun yi asarar adadi mai yawa. Muna jajantawa ƙasar mu, maza da mata. Batun Boko Haram wani mummunan tarihi ne a cikin wannan lokaci na ci gabanmu. Gwamnati na yin komai don ganin mun ciyar da ƙasarmu gaba. Amma waɗannan abubuwan da ba dole ba ne ke jawo mana koma baya. Amma za mu kawo karshen hakan.[10]

Harin dai ya zo ne kwana guda bayan ɗan majalisar dattawan Najeriya Ahmed Zanna ya yi ikirarin cewa ƙungiyar ƴan ta'addan, ta hallak fararen hula 135 a arewa maso gabashin Najeriya a wasu jerin hare-hare uku da aka kai, a makon da ya gabata.[11]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Minister: 75 dead in blast at nigerian bus station". Associated Press. 15 April 2014. Archived from the original on 16 April 2014. Retrieved 15 April 2014.
  2. "Nigeria violence: 'Seventy killed' in Abuja bus blasts". BBC News. 14 April 2014. Retrieved 14 April 2014.
  3. Ijagba, Gbenga Seun; Drew Hinshaw (14 April 2014). "Nigeria Bomb Blast Kills At Least 71". The Wall Street Journal. Abuja. Retrieved 14 April 2014.
  4. 4.0 4.1 Abrak, Isaac; Felix Onuah; Camillus Eboh; Tim Cocks (14 April 2014). "Nigerian bus station bombing kills 71 on edge of capital". Reuters. Retrieved 14 April 2014.
  5. 5.0 5.1 "How the Abuja Bomb was Planted + Survivors Recount Their Experience - Date360 | Naijablogger". Date360. 2014-04-15. Archived from the original on 2014-04-21. Retrieved 2014-08-26.
  6. Pflanz, Mike (14 April 2014). "Blast in Nigerian capital kills 71". The Daily Telegraph. Retrieved 15 April 2014.
  7. 7.0 7.1 "71 killed in a Bomb Blast at a Bus Station in Nigeria". IANS. news.biharprabha.com. Retrieved 14 April 2014.
  8. FAUL, MICHELLE (2014-04-19). "Islamist Militants Boko Haram Claim Deadly Nigeria Blast". Huffingtonpost.com. Retrieved 2014-08-26.
  9. Freeman, Collin (15 May 2014). "British-born Boko Haram member arrested over bomb attack". The Daily Telegraph. Retrieved 15 May 2014.
  10. "President Jonathan Cancels Trip To Ibadan; Visits Scene Of Blast". Channels Television. 14 April 2014. Retrieved 15 April 2014.
  11. "Nigerian senator: '135 civilians killed' in attacks". BBC News. 12 April 2014. Retrieved 15 April 2014.

Coordinates: 9°03′00″N 7°30′00″E / 9.0500°N 7.5000°E / 9.0500; 7.5000