Harin bom a Konduga, 2019

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harin Bom a kunduga, 2019
suicide bombing (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Kwanan wata 16 ga Yuni, 2019
Wuri
Map
 11°39′06″N 13°25′10″E / 11.6517°N 13.4194°E / 11.6517; 13.4194

A yammacin ranar 16 ga watan Yuni 2019, wasu ƴan ƙuna baƙin wake uku sun tayar da bam a ƙauyen Konduga da ke jihar Bornon Najeriya, inda suka kashe mutane 30 tare da raunata sama da 40.[1][2] Ɗan kunar bakin wake na farko ya afkawa masoya kwallon kafa da ke kallon wani wasa a gidan talabijin a zauren.[3] Maigadi ne ya hana shi shiga falon. An tafka zazzafar muhawara, inda ɗan kunar bakin waken ya tayar da bam din da ke jikinsa. Wannan harin dai shi ne harin kunar baƙin wake mafi muni a shekarar 2019 a Najeriya.[4] Ba da daɗewa ba, sauran biyun - dukansu mata ne[2] - sun tarwatsa kansu a kusa.[1]

Wai-wa-ye[gyara sashe | gyara masomin]

Garin Konduga ya sha fama da hare-hare a baya-bayan nan, da suka haɗa da kisan kiyashi a watan Janairun 2014 da kuma a watan Fabrairun 2014, harin ƙuna bakin wake sau uku a watan Fabrairun 2018 harwayau da wani harin kuna bakin wake a wani masallaci a watan Yulin 2018.[3]

A ranar 27 ga Yuli, 2019, wasu gungun da suka dawo daga jana'izar a Nganzai, jihar Borno, sun mutu sakamakon harbin da aka yi musu a harin jana'izar Nganzai. Akalla mutane 65 ne suka mutu. Babu dai Ƙungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma ƙungiyar Boko Haram mai kishin Islama ta kan aiwatar da kisan kiyashi, galibi a Borno.[5]

Alhakin kai harin[gyara sashe | gyara masomin]

Babu dai ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin, duk da cewa harin Konduga na ɗauke da alamomin na Boko Haram ne. Ɗaya daga cikin sansanonin kungiyar na nan kusa da Maiduguri.[6] Boko haram na kallon wasan kwallon kafa a matsayin wanda bai dace da Musulunci ba kuma gurbataccen tasirin kasashen yamma.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Suicide blast kills football fans in Nigeria" (in Turanci). 2019-06-17. Retrieved 2019-06-17.
  2. 2.0 2.1 Bukola Adebayo. "30 dead in triple suicide bomb blasts in Nigeria". CNN. Retrieved 2019-06-17.
  3. 3.0 3.1 "Nigeria suicide attack: Triple blasts kill at least 30 in Borno". www.aljazeera.com. Retrieved 2019-06-17.
  4. 4.0 4.1 "Triple suicide attack kills at least 30 in northeast Nigeria". Reuters (in Turanci). 2019-06-17. Retrieved 2019-06-17.
  5. "Suspected Islamists kill at least 65 in northeast Nigeria - state TV". Reuters. Retrieved 28 July 2019.
  6. "30 killed in Nigeria suicide bombing while watching TV match". ABC News (in Turanci). Retrieved 2019-06-17.