Jump to content

Harin bom a Potiskum, 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Harin bom a Potiskum
suicide bombing (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Rikicin Boko Haram
Ƙasa Najeriya
Kwanan wata 10 Nuwamba, 2014
Wuri
Map
 11°42′43″N 11°04′11″E / 11.7119°N 11.0697°E / 11.7119; 11.0697

A watan Nuwamba 2014, an kai wasu hare-haren ta'addanci sau biyu a garin Potiskum da ke jihar Yobe a Najeriya. Dukkan Hara-haren kwara biyu sun hada da; harin ƴan ƙuna baƙin wake, inda suka kashe aƙalla mutane 61 tare da jikkata wasu da dama. Ana dai zargin kungiyar Boko Haram a matsayin wadda ta kai hare-haren.

A kan ƴan Shi'a

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar 2014, wani ɗan ƙuna baƙin wake ya kashe aƙalla mutane 15 a wani hari da aka kai wa ƴan shi'a, a lokacin da suke tsaka da gudanar da tattakin tunawa da ranar Ashura. Kimanin mutane 50 ne suka jikkata a harin, yayin da jami’an tsaro suka harbe wasu biyar.[1][2][3]

A makarantar gwamnati

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 10 ga watan Nuwamba, 2014, kusan adadin mutane 46 ne suka mutu sannan 79 suka jikkata a wani harin kuma na ƙuna baƙin wake da aka kai a Potiskum, jihar Yobe, Najeriya. An kai harin ne a lokacin da dalibai suka taru a ɗakin taro na Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati. Maharin ya shiga makarantar sanye da kayan makaranta a matsayin basaja. Bayan harin, gwamnan jihar ya rufe dukkan makarantun gwamnati a yankin.[4][5]

 * Harin makaranta a jihar Yobe

  1. "Nigeria Shias in Potiskum hit by 'suicide attack'". BBC News. Retrieved 10 November 2014.
  2. "Suicide blast kills 29 in Nigeria, prison attack frees 144". Reuters. Retrieved 10 November 2014.
  3. AFP. "Blast hits Shia ceremony in Nigeria's Yobe". Retrieved 10 November 2014.
  4. "Suicide bomber kills 48 students in Nigeria". Yahoo News. 10 November 2014. Retrieved 10 November 2014.
  5. "Nigeria school blast 'kills 47 students' in Potiskum". BBC. 10 November 2014. Retrieved 10 November 2014.