Hikimomin Zantukan Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hausawa tun fil azal suna da salo iri-iri na maganganu cikin hikima kamar haka:[1]

1. Karin magana

2. Kirari

3. Habaici

4. Barkwanci

5. Zaurance

6. Shagube

7. Ba'a

8. Bakar Magana

9. Kacici-kacici

Karin Magana[gyara sashe | gyara masomin]

Karin magana wasu jerin kalmomi ne wanda ba kasafai suke nufin ainifin ma'anarsu ba. Wannan na nufin cewa ana sakaya ainihin ma'anar da kalma ke nufi. misali;

A bar kaza cikin gashinta

Idan aka lura da wannan magana ba wai ana nufin gaza cikin gashinta ba, a'a.. ana nufin cewa a rufa asiri

Kirari[gyara sashe | gyara masomin]

Kirari wasu lafuzza ne na hikima da hausawa kanyi don koda kawunansu ko wani mutum musamman idan bukatar hakan ya taso.

Habaici[gyara sashe | gyara masomin]

Habaici magana ce da hausawa kanyi cikin hikima don gayawa wani sako amma ba kai tsaye ba, a fakaice ake yinta watau a boyayyar manufa. Akanyi magana a fakaice da nufin wanda akeyi ma wa ya ji. Amma shi habaici idan ba da mutum akeyi ba, ba kasafai yake gane abinda ko wanda akeyi don shi ba.

Anfi yin habaici ga wanda ya aikata wani abu mai muni ko mara kyau. Misali;

Idan ana zargin mutum da sata ko ya taba yin sata, za'a iya masa habaici da cewa 'shegun barayin nan sun dame mu da sata" ko makamancin hakan

Barkwanci[gyara sashe | gyara masomin]

Barkwanci na nufin ba'a wacce ake yi a cikin zance, kuma acikin raha da nishadi. Barkwanci ba'a ce wacce hausawa da makwabtansu suka amince da ita don jawo raha a tsakaninsu. Barkwanci ba'a ce mai cikakken 'yanci da hujja kuma ta kasu kashi biyu;

Barkwanci na tsakanin Kabilu[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan kalan barkwanci ne tsakanin kabilu guda biyu wanda mafi akasarin wanna barkwanci shine dalilin yaki da sukayi tsakaninsu a zamanin da ko kuma jin dadin zamantakewarsu da juna sai su riqa zolayar junansu. misali; tsakanin Katsinawa da Hadejawa, ko tsakanin Gobirawa da Yarbawa, ko tsakanin Zage-zagi da Kanawa.

Barkwanci na masu sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan wani irin yanayi ne na ba'a da tsokanan juna tsakanin 'yan kasuwa ko masu sana'a da ke da dangantaka. Misali,

Barkwanci tsakanin masunta da mahauta - a irin wannan sana'oi daya a ruwa suke samunsu, dayan kuma a tudu,

Barkwanci tsakanin makafi da kutare

Bibiyar Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Gusau, Sa'idu Muhammad (1996-). Makad̳a da mawak̳an Hausa. Kaduna. ISBN 978-31798-3-7. OCLC 40213913.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Gusau, Sa'idu Muhammad (1996-). Makad̳a da mawak̳an Hausa. Kaduna. ISBN 978-31798-3-7. OCLC 40213913.