Kirari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kirari wani irin abu ne mai matukar muhimmanci dangane da al’adar bahaushe, musamman a bangaren waka ko a wake. Ana yin shi a cikin waka ko a wajen taron biki irin su nadin sarauta ko a mahauta (gurin sayar da nama) ko filin dambe ko wajen farauta ko wasan tauri da dai sauransu. Kirari Nau’i ne na yabo, amma ya bambanta da yabo domin shi tsagwaron zuga ne ko kambamawa. Yawanci, mutum daya ko wasu mutane ne suke yi wa wani mutum daya kirari, kuma mutum daya ake yi wa kirarin a lokaci guda. Haka kuma, mutum zai iya yi wa kansa kirari, kamar yadda ’yan dambe ko ’yan kokawa ko kauraye ke yi.

Kirari dai ya kumshi kalmomi kamar: “Kai ne wane dan wane jikan wane! Babu kamar ka! Ba a ja da kai! Kai ne ka yi abu kaza da kaza!” A wani kirarin, a kan kara da kalmomi na tsoratarwa ko firgitarwa saboda abokan gaba, misali a kira mutum Dodo. Wata sa’a har ashariya ko batsa akan watsa a cikin kirari. Shi ma mai koda kansa da kansa din hakan yakan yi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]