Hula
hula | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | headgear (en) |
Fabrication method (en) | Dinkin hula |
Hula Wata sutura ce da ake sawa a kai. A al'adar Malam Bahaushe sa hula na daya daga cikin cikar kamalar ɗa namiji da suranta girma. Garuruwan da suka shahara a ɗinkin hula su ne kamar haka, Borno da Katsina da Paki. Hula suna ne na "tilo" jam'i kuma "Huluna". Kuma hula tana da mutukar muhimmanci a wajen mutane, musamman ma a Kasar Hausa, kuma tana nuna cikar kamala "cikar ado a wurin Malam Bahaushe sai da hula".
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Hula dai ta samo asali ne tun a ƙarnin baya, inda mutane musamman ma dattawa suka fi amfani da ita domin sanya ta a kai, hula tana kara nuna mahimmanci ga mutane a wasu ƙabilun inda wasu kuma ke sanya ta domin ado. Hula kala-kala ce kuma a Nijeriya kusan kowane yanki da yadda suke sa hula. Kuma maza su ne aka fi sani da sana'ar ɗinkin hula musamman ƴan Maiduguri.[1] [2]