Ibrahim Adamu Kolo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ibrahim Adamu Kolo
Rayuwa
Haihuwa Mokwa, 1956
Mutuwa 2018
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Farfesa Ibrahim Adamu Kolo (an haife shi a ranar 29 ga watan Oktoba shekara ta 1956 - ya rasu a ranar 3 watan Nuwamba shekara ta 2018) ya kasance masanin ilimin Neja. Ya rayu a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja .

Ya halarci makarantar firamare ta UMCA da makarantar firamare ta St. Johns Anglican. Ya tafi makarantar sakandare a Kwalejin Gwamnati ta Bida kuma ya samu digiri na farko a Kwalejin Ilimi da ke Sakkwato, da Jami’ar Bayero, da Jami’ar Jos.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kasance malami a Kwalejin Ilimi, Jami'ar Bayero ta Kano . Ya yi aiki a matsayin Provost na Kwalejin Ilimi ta Jihar Neja, daga shekara ta 2001, zuwa shekara ta 2010.

Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida University, Lapai, daga shekara ta 2010, zuwa shekara ta 2015. Kwamishinan Ilimi mai zurfi Peter Sarki ya sanar da nadin Kolo a matsayin Mataimakin Shugaban Jami'ar, yana mai jaddada bukatar tsabtace jami'ar da kuma gyara lalacewar harkokin mulki. [1]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Kolo ya mutu a Minna yana da shekara 62 bayan gajeriyar rashin lafiya. Janar Ibrahim Babangida ya bayyana mutuwar Kolo a matsayin "babban rashi ne ga bangaren ilimin jihar Neja da ma Najeriya baki daya".

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ibbulapai vc, "ibbulapai new vc" Archived 2019-06-27 at the Wayback Machine, Daily Trust, January 2010

Madogara[gyara sashe | gyara masomin]

  • Empty citation (help)