Ibrahim Dasuki Jalo-Waziri
Ibrahim Dasuki Jalo-Waziri | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 13 ga Afirilu, 1971 (53 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Ibrahim Dasuki Jalo-Waziri (an haife shi ranar 13 ga watan Afrilun, 1971). shine Shugaban Matasa na Kasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jam’iyya mai mulki a Najeriya. Tare da aikin siyasa wanda ya shafe shekaru 12, Ibrahim ya mallaki zaɓaɓɓun ofisoshi da muƙaman siyasa.[ana buƙatar hujja]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ibrahim a garin Maiduguri a ranar 13 ga watan Afrilu, shekara ta 1971 ga (marigayi) Sanata Ibrahim Jalo-Waziri da Hajiya Adama Modibbo. Mahaifinsa ya kasance Shugaban Majalisar Wakilai daga shekara ta alib 1960 zuwa shekara ta alib 1966,[1] kuma ya yi sanata tsakanin shekara ta alib 1979 da shekara ta alib 1983.
Dan asalin Ƙaramar Hukumar Gombe ne a Jihar Gombe, Ibrahim ya fara karatu ne a shekara ta 1978 a makarantar Firamare ta Tudun Wada, Gombe. A shekara ta 1983, ya zarce zuwa Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (wacce take garin Gombe), inda ya sami takardar shaidar SSCE a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, ya shiga Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Gombe, kuma ya sami damar kammala karatu na NCE a Ilimin Kasuwanci a shekara ta 1993. Ya kuma ciga ba da karatun sa, a tsakanin 1995-2000, ya kasance dalibi a Jami'ar Ahmadu Bello, daga nan ne ya sami digiri na farko a fannin Ilimin Kasuwanci. A cikin shekara ta 2005, ya sami digiri na Biyu (MBA) daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi.
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan kammala karatunsa daga Jami'ar Ahmadu Bello a shekara ta 2000, Ibrahim ya shiga aikin bautar kasa (2000-2001), wanda a lokacin kamfanin inshora na tsakiya (CICO),Jos, shi neyayi aiki na farko.
A shekara ta 2003, aka naɗa Ibrahim Sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe.[ana buƙatar hujja] Ya kuma sami mukamin siyasa a matsayin Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Jihar Gombe na wancan lokacin, Danjuma Goje, a cikin wannan shekarar.
A shekarar 2004, ya shiga takarar shugabancin karamar hukumar Gombe - wanda ya ci zaben - kuma ya ci gaba da wannan matsayin har zuwa 2007. A 2007, an rusa hukumomin zartarwa na kananan hukumomi; duk da haka, ya fito a matsayin shugaban riko kwarya a shekarar 2008, an sake zaben shi a hukumance a matsayin shugaban zartarwa na Karamar Hukumar Gombe. A lokacin wa'adinsa na biyu, an zabi Ibrahim Shugaban Kungiyar Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON), kungiyar da ta kunshi dukkan shugabannin kananan hukumomi 774 na fadin Najeriya.
A shekarar 2011, ya tsaya takarar wakiltan cun Mazabar Tarayya ta Gombe / Kwami / Funakaye a Majalisar Wakilai ta Tarayya, amma bai yi nasara ba.
A shekarar 2014, ya zama Shugaban Matasa na Kasa na Jam’iyyar All Progressives Congress.
Tsayawa a matsayin Shugaban Matasan APC
[gyara sashe | gyara masomin]Fitowar Ibrahim a matsayin Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na Kasa ya kasance cikin rikici, saboda labaran da ake zargin Jam’iyyar PDP mai mulki ke daukar nauyin sa na nuna shakku kan shekarun sa. Hakan ya kasance, sasantawa cikin hanzari daga jam'iyar APC da kungiyoyin matasa a cikin jam'iyyar suka yi masa kawanya don ba shi goyon baya.
A matsayinsa na shugaban matasa na jam'iyar APC,Ibrahim ya sami damar daidaita tsarin matasa na APC ta hanyar samar da kyakkyawar alakar aiki tsakanin shugabannin matasan, kamar yadda yake kunshe a cikin tsarin jam'iyyar na hukuman ce, da kungiyoyin matasa masu alaƙa da ikon tattara samarin Najeriya zuwa jam'iyyar. Sannan kuma memba ne na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na APC, inda yake shugabantar matasa kuma yana aiki tare da sauran shugabannin matasan APC kamar su Ismail Ahmed, Sesan Sobande, Damilola Elemo da Rinsola Abiola.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jam'iyyar All Progressive Congress
- John Odigie Oyegun
- Mohammed Danjuma Goje
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ The Europa World Year Book 1965