Mohammed Danjuma Goje
![]() | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2003 - Mayu 2011 ← Abubakar Habu Hashidu - Ibrahim Hassan Dankwambo →
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Cikakken suna | Mohammed Danjuma Goje | ||||||||
Haihuwa |
Acre (en) ![]() | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Ƙabila | Hausawa | ||||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Fillanci | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan/'yar siyasa | ||||||||
Imani | |||||||||
Addini | Musulunci | ||||||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Senata Mohammed Danjuma Goje (an haife shi a ranar 10 ga watan Oktoba na shekara ta alif 1952), a Pindiga, Akko,Jihar Gombe an zaɓe shi gwamnan Jihar Gombe a shekara ta 2003 ƙarƙashin jam'iyar PDP, ya kama aiki daga ranar 29 ga watan Mayu, shekara ta 2003, ya sake cin zabe a karo na biyu a shekara ta 2007 ya kuma kammala a shekarar 2011. A yanzu ɗan jam'iyar All Progressives Congress (APC) kuma sanata mai ci daga Jihar Gombe.[1]
A zaɓen watan Afrilu na shekara ta 2011, Mohammed Danjuma Goje ya nemi takarar zama sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya karkashin tikitin jam'iyar PDP. Ya karanta kimiyyar Siyasa a Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya taba zama dan majalisar Jihar Bauchi daga shekara ta alif 1979 zuwa shekara ta alif 1983. Goje ya rike Sakatare a National Institute For Medical Research dake Yaba Jihar Lagos, a shekara ta 1984-1989. Ya kafa ta shi kamfanin mai suna, Zaina Nigeria Ltd, a shekarar alif ta 1989 zuwa shekara ta 1999. Ya zama kamfanin suna ne daga sunan Mahaifiyarsa, Hajiya Zainab. Danjuma Goje ya nemi takarar kujerar sanata a Nigerian National Assembly a shekara ta alif 1998 daga nan ya zama Minister of State, Power and Steel daga shekarar alif ta 1999-2001 karkashin Shugaban cin Olusegun Obasanjo.[2].
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
.
- ↑ cite news |first = Ayuba |last = Hassan |title = Governor Danjuma Goje @ 55 |url = http://www.leadershipnigeria.com/product_info.php?products_id=15999 |work = Leadership |publisher = Leadership Newspapers Group Limited, Abuja |date = 2007-10-23 |accessdate = 2007-10-23 |deadurl = yes |archiveurl = https://web.archive.org/web/20071216103347/http://www.leadershipnigeria.com/product_info.php?products_id=15999 |archivedate = 2007-12-16 |df =
- ↑ cite web |url=http://www.vanguardngr.com/2011/04/presidential-contests-pdp-set-for-repeat-success-in-gombe/ |work=Vanguard |title=Presidential contests: PDP set for repeat success in Gombe |date=April 14, 2011 |author=John Bulus |accessdate=2011-04-21