Idakwo Ameh Oboni II

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Idakwo Ameh Oboni II
Rayuwa
Haihuwa 1948
Mutuwa 27 ga Augusta, 2020
Sana'a

Idakwo Michael Ameh Oboni II (1948 - Agusta 27, 2020)[1] ya kasance Sarki na 27, Àtá Ígálá (masarauta mafi girma) na Masarautar Igala da ke a Tsakiyar Najeriya.[2][3]

Rayuwa da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Oboni II a shekarar 1948. A 1960, ya kammala karatunsa na firamare a Saint Boniface da ke Idah. Daga nan ya ci gaba zuwa Kwalejin Saint Augustine, Kabba, inda ya kammala a 1967.[4] Daga nan ya wuce Kaduna Polytechnic har wayau ya kammala karatunsa da satifiket na shedar Estate Management a shekarar 1980.[4]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Daga nan ya shiga aikin sojan saman Najeriya a shekarar 1968 ya bar aikin a radin kansa a shekarar 1974. Bayan nan ya yi aiki a matsayin jami’in duba filaye a ma’aikatar filaye a tsohuwar jihar Kwara sannan ya bar aiki a shekarar 1975 don neman ilimi. A shekarar 1981, ya fara Aiki a hukumar raya babban birnin tarayya (FCDA) kuma a tsawon shekaru, ya kai matsayin mataimakin darakta, inda ya yi ritaya a shekarar 2006.[4]

Mulki[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan mutuwar 26th Àtá Igala Àtá Àlíì Ọ̀chẹ́ja Òtúlúkpé Ọ̀bàje a shekara ta 2012,[5] An zaɓi Àám̀ gaba ɗaya daga cikin gidaje huɗu masu mulki a Anɛ Igálá a matsayin magajin sarauta. An miƙa naɗin nasa ga Sarakunan Igalamela tara (9) a matsayin wani ɓangare na tsarin gargajiya al'adar masarautar. Masu sarauta sun amince da naɗin nasa don aikawa zuwa ga Achadu oko-Ata (Firayim Minista Igala).[6] An miƙa amincewar sa da firaministan Igala ya yi ga majalisar gargajiya ta jihar Kogi daga karshe gwamnan jihar kogi Capt Idris Ichala Wada ya amince da shi.[7] Ya furta cewa shi ne Ata na farko da ya auri mace ɗaya a tarihin ƙasar Igala.[4]

Da zuwan gwamnatin Buhari a Najeriya, HRM Ameh Oboni II a shekarar 2016 a garin Idah, yayin bikin cikar sa karo na uku kan ƙaragar mulki, ya ɗora wa shugaban kasa "ya fara canza sheka a jihar Kogi".[8]

Bayan zaɓen 2019 da tashe-tashen hankula suka biyo bayan zaɓen 2019, ƙungiyar Àtá Igálá ta la'anci waɗanda suka aikata ta'addancin zaɓe a jihar.[9]

Dabi'u[gyara sashe | gyara masomin]

An bayyana shi a matsayin mutum mai son zaman lafiya kuma mai ba da shawarwari masu kyau da kuma sanannen gaskiya. Dansa, Prince Ocholi Idakwo ya bayyana shi a matsayin "mutum mai aiki kuma mai kishin raya al'adun Igala".[10]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Rahotanni sun ce ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis 27 ga watan Agustan 2020 bayan ɗan gajeran mulki na kimanin shekaru takwas, wanda ya fara bayan rasuwar magabacinsa wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 52.[11] Oboni II ya rasu ne a wani asibitin Abuja bayan da aka yi masa tiyatar da ba'a yi nasara ba.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Attah of Igala,Dr.Aliyu Obaje is dead". Newsdiaryonline. July 16, 2012. Retrieved 11 October 2013.
  2. "Buhari mourns Attah Igala, Michael Oboni II". Premium Times Nigeria. August 30, 2020. Retrieved September 25, 2020.
  3. Moribirin, Rosemary (August 27, 2020). "Breaking: In Kogi, Attah of Igala is dead". Blueprint. Retrieved September 25, 2020.
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 "Ameh, Attah Igala, dies during operation in Abuja". The Cable. August 27, 2020. Retrieved September 25, 2020.
  5. "Attah Igala, Aliyu Obaje dies at 102 | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2012-07-17. Retrieved 2022-03-03.
  6. "Intrigues as race for Attah Igala stool heats up". Daily Trust (in Turanci). 2020-11-15. Retrieved 2022-09-18.
  7. Ottah, Gabriel Alhassan (2015-10-27). "African Culture and Communication Systems in the Coronation of Ata Igala, North- Central Nigeria". AFRREV IJAH: An International Journal of Arts and Humanities (in Turanci). 4 (3): 208–228. doi:10.4314/ijah.v4i3.18. ISSN 2227-5452.
  8. Sule, Itodo Daniel (March 30, 2016). "Nigeria: Attah Igala Tasks Buhari On Change Mantra". All Africa. Daily Trust (Abuja). Retrieved September 25, 2020.
  9. "Dr Michael Idakwo Ameh Oboni 11 Attah Igala places ancestral curse on perpetrators of electoral violence". The Guardian. March 3, 2019. Retrieved September 25, 2020.
  10. Olaniyi, Muideen (August 29, 2020). "Buhari: Late Attah Igala, Ameh Oboni II, Was A Man Of Peace". Daily Trust. Retrieved September 25, 2020.
  11. "Attah of Igala, Idakwo Ameh Oboni II, passes away". KAFTANPost. August 27, 2020. Retrieved September 25, 2020.