Idris Legbo Kutigi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Idris Legbo Kutigi
Chief Justice of Nigeria (en) Fassara

2007 - 2009
Rayuwa
Haihuwa Arewa maso yammacin jiha, 31 Disamba 1939
ƙasa Najeriya
Mutuwa Landan, 21 Oktoba 2018
Karatu
Makaranta School of Oriental and African Studies, University of London (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello
Kwalejin Barewa
Sana'a
Sana'a mai shari'a

Idris Legbo Kutigi ya rayu daga 31 ga watan Disamba 1939 zuwa 21 ga watan Oktoba 2018 ya kasance lauyan Nijeriya kuma alƙali.[1] Ya riƙe shugaban Alkalai a jihar Niger da kuma Babban kamishinan a Hukumar Shari'a kafin yazamo Alkali a Babban Kotun Najeriya,[2] sannan daga bisani yazama alkali a kotun koli ta Nijeriya a shekara ta 1992. Yakaiga matsayin Shugaban Alkalai daga 30 ga watan Janairu 2007 har zuwa 30 Disamba 2009.[3]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haife Kutigi a 31 Disamba 1939 a tsohuwar kasar mulkin turawa wadda itace Nijeriya a yanzu, ya rasu a 21 ga watan Oktoba 2018, (wanda a yanzu take karkashin karamar hukumar Lavun , Jihar Niger). Kutigi ya halarci makarantar firamare a Kutigi kuma ya yi karatunsa na sakandare a Bidda.[3] Daga bisani ya koma zuwa Government College (wanda a yanzu akafi sani da Barewa College), sannan bayan ya gama ya koma Jami'ar Ahmadu Bello duka a Zariya, Jihar Kaduna. Daga na ya bar kasannan zuwa London inda yayi karatu a School of Oriental and African Studies, University of London da kuma makarantar lauyoyi na Gibson and Weldon, kafin ya dawo ya halarci makarantar lauyoyi na Najeriya da ke Lagos, jihar Lagos. Sannan daga bisani an kirashi zuwa kungiyar lauyoyin Najeriya a shekarar 1964.[4]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Kutigi ya rike matsayin Solicitor General kuma babban sakatare na jihohin arewa maso yamma a 1976, daga bisani kuma ya zamo attorney general kuma commissioner na shari'a na jihar Niger, sannan kuma darekata na amsan karan jama'a, ya rike wadannan makamai uku a lokaci daya a tsakanin 1976- 1977, kafin ya zama babban alkalin High Court daga bisani aka nadashi alkalin Kotun Koli na Najeriya (Supreme Court) a 1992 sannan shugaba Olusegun Obasanjo ya bashi matsayin alkalin alkalan Najeriya a shekara ta 2002 don ya gaji matsayin daga hannun Salihu Alfa Belgore ne a matsayin shugaban alkalan Nijeriya. Balgore ya ajiye aiki a ranar 17 January 2002, inda Kutugi ya amsa matsayin a ranar 30 ga watan Januairun 2002, bayan majalisar dattijai sun tantance shi.[5]Ya gyara dokar "1979 Fundamental Human Enforcement Procedure Rules" wanda daga baya ta zamo Fundamental Rights (Enforcement Procedure) Rules na shekara ta 2009.

Kutigi ya ajiye aiki shima a ranar 30 ga watan Decemban 2009 a lokacina da ya kai shekarun ajiye aiki wato shekaru 70, inda ya rantsar da magajin kujerarsa Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu a maimakon shugaban kasa, saboda shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua na jinya rashin lafiya.[6]Daga nan ya dawo ya cigaba da aiki a matsayin alkalin High Court har zuwa mutuwar sa a watan Octoban 2018.[7]Kutugi ya cigaba da halartar taron manya na kasa (Council of State meeting) wanda akeyi don ra'ayin shugaban kasa.[8]

A cikin shekara ta 2014 ne shugaba Jonathan Goodluck ya nadashi matsayin chairman na National Conference akan harkokin tsarin mulkin kasa.[9][10]Anyi maraba da wannan matsayi da aka bashi daga kowanne bangare saboda gaskiyar sa da rashin nuna son zuciya a harkokin sa. A ranar 12 ga watan Yunin 2014 ya shiga tsakanin 'yan siyasan arewa da kudu wadanda suka kacema da fada akan tunawa da wadanda suka mutu a lokacin zaben shekarar 1993.[11]

Rayuwarsa[gyara sashe | gyara masomin]

Kutugi yana da 'ya'ya 18 da jikoki sama da 40. Ya mutu a Birnin London dake Kasar Ingila bayan rashin lafiya na dan lokaci.[12]

Akwai wata unguwa a birnin tarayya da aka sanya wa sunan shi a watan Aprelun, 2015 don tunawa da shi.[13]Sannan akwai babban wurin taro na Justice Idris Legbo Kutigi International Conference Centre da ke Minna wanda akayi don tunawa da shi.[14]

An umurci kada tutocin Najeriya don karramawa a yayin mutuwar sa kuma anyi hutun kwanaki 7 don tunawa da shi. An bude littafin jimaminsa a babban kotun koli na Najeriya.[15]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Justice Kutigi and his judicial legacy". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 30 October 2018. Retrieved 6 March 2022.
  2. editor (21 October 2018). "Former CJN, Idris Kutigi, Dies at 78". THISDAYLIVE. Retrieved 27 May2020.
  3. 3.0 3.1 "Hon. Justice Idris Legbo Kutigi CON". Scn.gov.ng. Supreme Court of Nigeria. 1 February 2007. Retrieved 4 May 2007.
  4. "Confab: Kutigi is qualified—Sagay, Falae, Afenifere, others". Vanguard News. 5 March 2014. Retrieved 21 October 2018.
  5. "Behold The New CJN". Independent Online. Independent Newspapers. Retrieved 4 May 2007.
  6. "Mike Ozekhome (1 February 2010). "That Oath By Katsina-Alu". ThisDay. Retrieved 16 February2010.
  7. "Court Remands 2 Over Alleged N137m Fraud — Leadership Newspaper". Leadership Newspaper. Retrieved 21 October 2018.
  8. "Jonathan, Babangida absent but Obasanjo attends council of state meeting". The Cable. 22 February 2018.
  9. "Ex-Chief Justice Idris Kutigi Is Dead". The Will Nigeria. Retrieved 21 October 2018.
  10. "Gov. Bello congratulates Justice Idris Kutigi at 76". PM News Nigeria. Retrieved 21 October2018.
  11. "June 12 and question of Buhari's motive". Vanguard News. 14 June 2018. Retrieved 21 October 2018.
  12. "Ex-CJN Kutigi dies in London". Premium Times Nigeria. 21 October 2018. Retrieved 21 October2018.
  13. "FG names Abuja streets after Jonathan, Sambo, Muazu, Atiku, Dangote, others". Vanguard News. 28 April 2015. Retrieved 21 October 2018.
  14. "When literary and art festival debuted in Minna – Daily Trust". Daily Trust. 29 September 2018. Retrieved 21 October 2018.
  15. "Onnoghen, Atiku Mourn Kutigi". This Day. 21 October 2018. Retrieved 21 October 2018.