Jump to content

Ike Ibenegbu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ike Ibenegbu
Rayuwa
Haihuwa Najeriya, 22 ga Faburairu, 1986 (38 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
El-Kanemi Warriors F.C.2005-2006
Nigeria national beach soccer team (en) Fassara2006-2009105
Enyimba International F.C.2007-2008
Heartland F.C. (en) Fassara2008-2014
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya2012-
Warri Wolves F.C.2014-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Tsayi 1.74 m

Bartholomew Ikechukwu Ibenegbu (an haife shi a ranar 22 ga watan Fabrairun shekara ta alif dari tara da tamanin da shida 1986), wanda ake kira Mosquito, dan wasan tsakiya ne na Najeriya wanda ke buga wa Kulob din Enugu Rangers . [1]

Kafin Heartland, ya buga wa Enyimba FC da El-Kanemi Warriors, inda ya jagoranci Gasar Firimiya ta Najeriya ya zira kwallaye a shekara ta 2006 tare da kwallaye goma.[2]

Ayyukan kasa da kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ibenegbu ya taka leda a Kungiyar kwallon kafa ta bakin teku ta Najeriya tun shekara ta 2006. [3] An kira shi zuwa sansanin Yan kasa da shekaru 23 na shekarar 2007 kafin Wasannin Olympics na Beijing amma bai shiga tawagar karshe ba.[4] An kira shi zuwa sansanin don Babban kungiyar a gaban gasar cin Kofin Kasashen Afirka na 2010, daya daga cikin yan wasa uku kawai na gida da suka yi hakan.[5]Ya fara bugawa a matsayin mai maye gurbin a wasan sada zumunci na Janairun shekarar 2012 da Angola .

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin Hadin waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Ike Ibenegbua FootballDatabase.eu