Ishaku Abbo
Ishaku Abbo | |||
---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - 16 Oktoba 2023 ← Binta Masi Garba District: Adamawa North | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Ishaku Elisha cliff Abbo | ||
Haihuwa | Jihar Adamawa, 2 Mayu 1976 (48 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Peoples Democratic Party All Progressives Congress |
Ishaku Elisha Abbo (An haife shi a Mubi North, Nigeria ) ɗan siyasan Najeriya ne . Shine ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta arewa a jihar Adamawa a majalisar dokokin Najeriya karo na 9 . A halin yanzu ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne.
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 23 ga watan Fabrairun na shekara ta 2019, an zaɓi Abbo a matsayin Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, bayan da ya samu kuri’u 79,337 yayin da Sanata mai ci, Binta Masi Garba .
Rigima
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Mayun 2019, Abbo ya ci zarafin wata mata a wani shagon kayan manya da ke Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa mai shagon ne ya kira Abbo da suna "dan dunk" a lokacin da ya shiga tare da wasu mata uku domin sayan kayan wasan yara. Hotunan faifan bidiyo da Premium Times ta samu sun nuna Abbo ya mari mai shagon a lokacin da jami'an tsaronsa ke yunkurin cafke mai shagon. Abbo bayan ya afkawa mai shagon ya yi ikirarin cewa “ya damu matuka da rashin lafiyar daya daga cikin ƴan matan nasa ba zato ba tsammani” kuma ya zargi mai shagon da sanya wa na’urar sanyaya iska guba.
A watan Satumbar 2020, babbar kotun birnin tarayya, Maitama, ta yi watsi da karar saboda rashin tuhuma da ƴan sanda suka yi. A watan Satumban 2020, an kai karar zuwa wata kotun majistare da ke Zuba, Abuja inda aka sake nazarin karar tare da faifan bidiyo na lamarin. An samu Abbo da laifi kuma an umarce shi da ya biya Osimibibra Warmate, mai shagon Naira miliyan 50.
Kyauta
[gyara sashe | gyara masomin]Abbo ya kasance wanda ya samu lambar yabo ta 'Beacon of Hope' wanda The Adamawa Celebrities & Achievers Awards ta bayar a shekarar 2019.