Ishaq Bello
Ishaq Bello | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Zariya, 5 ga Janairu, 1956 (68 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | masana da mai shari'a |
Mai shari’a Ishaq Usman Bello (An haife shi a ranar 5 ga watan Janairun shekarata alif 1956) masanin shari’a ne na Najeriya, kuma babban alkali na birnin tarayya Abuja, kuma dan takarar da Najeriya ta tsayar a zaben 2020 na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague na kasar Netherlands. An fi saninsa da ƙoƙarinsa na rage cunkoso a gidajen yari da dama, waɗanda a yanzu aka fi sani da wuraren gyarawa, a Nijeriya.
A farkon aikinsa, Bello ya kasance, bisa dalilai na hukuma, a waje da kuma kan benci. A watan Nuwamba shekarata alif 1984, ya bar aikin sirri ya zama lauyan gwamnati a ma’aikatar shari’a ta jihar Kaduna kuma sai da ya kai shekara ta gaba ya zama majistare.
Daga nan ya bar benci bayan ya yi aiki a matsayin majistare na tsawon shekaru biyu. An canza shi na wani dan lokaci aka nada shi shugaban sashen farfado da shari’a a bankin Universal Bank of Nigeria plc a lokacin tsakanin shekarata alif 1987 zuwa shekarata alif 1989..
A shekarar alif 1993 ya shiga hukumar kula da koguna da ke Minna a jihar Neja a matsayin sakatare da mai ba da shawara kan harkokin shari’a. A shekarar alif 1995 ne wa’adinsa na mashawarcin shari’a ga hukumar ya kare, bayan haka ne Bello ya fara zama lauyan gwamnatin tarayya bayan nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin babban magatakarda na kotun koli ta Najeriya.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ishaq Usman Bello a garin Zariya dake jihar Kaduna a shekarar 1956. Ya yi shekarunsa na farko a St Bartholomew Primary Wusasa da ke Zariya a shekarar 1965 kafin ya koma L.E.A Primary School T/Jukun Zaria, inda ya samu takardar shaidar kammala makaranta a shekarar 1972.
Bayan ya samu satifiket din sai ya tafi jihar Katsina, inda ya samu shaidar kammala karatunsa na makarantar West Africa (WASC) a shekarar 1976. Daga nan ya koma Zariya bayan shigarsa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), inda ya kammala karatunsa na digiri na biyu (LLB) a shekarar 1982. An kira shi lauya a shekarar 1983.
Bello ya yi digirin digirgir (LLD Honoris Causa) a Jami’ar Caribbean.
manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]https://njc.gov.ng/council/profile/19 Archived 2020-11-28 at the Wayback Machine
https://guardian.ng/news/fct-cj-moves-to-clear-backlog-of-cases-releases-eight-prisoners/ Archived 2023-03-16 at the Wayback Machine