Ismail ibn Musa Menk
Ismail ibn Musa Menk | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Harare, 27 ga Yuni, 1975 (49 shekaru) |
ƙasa | Zimbabwe |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Musulunci ta Madinah |
Harsuna |
Larabci Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mufti (en) , mai yada shiri ta murya a yanar gizo da motivational speaker (en) |
Muhimman ayyuka | Mufti Menk (en) |
Mamba | The Council of Islamic Scholars of Zimbabwe (en) |
Fafutuka | Ash'ari (en) |
Sunan mahaifi | Mufti Menk |
Imani | |
Addini | Musulunci |
muftimenk.com |
Ismail ibn Musa Menk (an haife shi a shekara ta 1975) dan kasar Zimbabwe ne, mai waazi ne na addinin musulunci[1]. Shi ne Babban shugaban al'ummar Musulmi ta Zimbabwe, kuma shugaban sashen fatawa na Majalisar Malaman Musulunci ta Zimbabwe. An nada Menk daya daga cikin Musulmai 500 Mafi Tasiri a Duniya ta Cibiyar Tunanin Musulunci ta Royal Aal al-Bayt da ke Jordan a cikin 2013, 2014[2] da 2017[3].Ya sha fama da cece-kuce da dama a lokacin aikinsa, lamarin da ya sa aka dakatar da shi daga shiga cikin kasashe irin su Singapore da Denmark.
Rayuwarshi da karatunshi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Menk a ranar 27 ga Yuni 1975 a Salisbury ga iyayensa wadanda suke Musulman Indiya na Gujarati daga al'ummar Bharuchi Vohra Patel[4]. Shi da ne ga Maulana Musa Ibrahim Menk, mai wa’azin musulmi a kasar Zimbabwe. Mufti Menk yana iya yaren Gujarati da Urdu kuma ya fara karatunsa tare da mahaifinsa, yayi haddar Alqur'ani da koyi Larabci. Ya tafi makarantar sakandare ta St. John (Harare). Sannan ya kammala karatunsa na addini da kuma karatun Mufti daga Kantharia Darul Uloom da ke Gujarat a Indiya. haka kuma a Madina. An tabbatar da cewa Menk cikakken Deobandi ne haka nan basaalafiyye ne.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Mufti Menk Arrives in Gambia". 2 November 2018. Archived from the original on 11 April 2019. Retrieved 13 June 2021.
- ↑ "The 500 Most Influential Muslims 2017" (PDF). Royal Islamic Strategic Studies Centre.
- ↑ "The 500 Most Influential Muslims 2013–14" (PDF). Royal Islamic Strategic Studies Centre. Archived from the original (PDF) on 29 July 2018. Retrieved 25 March 2018.
- ↑ "Bharuchi Vahora Patel – In Africa – Gujarati Writers' Guild UK". www.mahek.co.uk. Retrieved 17 January 2023