Istihara
Istihara ko Istikhara wata sallah ce ta Nafila da akeyi domin neman za'bin Allah madaukakin sarki game da wasu al'amura guda biyu da bawa yake neman zabin Allah a cikin ɗaya daga cikinsu, cikin dukkan abubuwan da zai Aikata. Istihara ibadace (addu'ace) kuma Annabi muhammadu (s.a.w) shine ya koyar da yadda ake yin ta, saboda mahimmanci na wannan ibada manzon Allah (s.a.w) shi ya koyarda ita da kanshi. Sahabi jabir (r.a) yana cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yakasance yana koyar damu istihara Kamar yadda yake koyar damu Sura acikin Al'ƙur'ani", kunga wannan yake nuna mana ashe ita itikhara annabi ne ya koyar da ita bawai kowa gaban kansa zeyi kawai yaje ya aikata abinda yaga dama a matsayin istkhara ba.
Lokacin sallar istihara
[gyara sashe | gyara masomin]Da farko dai Ita sallar istikhara bata da wani keɓantaccen lokaci da akace dole sai a lokacin mutum zeyi a'a duk lokacin da wani al'mari ya bijirowa mutum da safe ne ko da rana da yamma ne ko da daddare dukkan waɗannan lokutan ya halatta mutum yayi sallar neman zabin Allah a cikinsu, misali koda a lokutan da aka hana sallah ne indai sai kuma wani al'amari ya bijirowa mutum kuna yana bukatar ya nemi zabin Allah a cikin lamarin to ya halatta yayi sallar istikharar domin neman zabin Allah ko da a lokutan da aka haramta yin sallah ne kamar yadda malamai suka ce.
Yadda ake sallar istihara
[gyara sashe | gyara masomin]- Niyya kamar yadda muka sani a cikin shahararren hadisin Amirul muminin Sayyadi umar bin khaɗɗab cewa manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace dukkan ayyuka basa yiwuwa/tabbatuwa sai da niyyoyinsu. To kamar hakane itama sallah istikhara bata tabbatuwa sai da niyya. Bayan mutum yayi niyyar sallar istikhara sai yaje yayi alwala kamar yadda yake sallah bata ingantuwa sai da alwala, Amma idan mutum yana da alwala a lokacin da yake son yin istikharar kawai zeyi sallar ne babu bukatar sai ya sake sabuwar al'wala.
- Sallah Mutum zeyi Sallah Raka'a biyu.
surorin da'ake karantawa cikin sallar
- Raka'a ta farko mutum ze karanta suratul fatiha da suratul kafirun
- Raka'a ta biyu kuma mutum ze karanta suratul fatiha da suratul ikhalas.
Lokacin da ake karanta addu'ar
[gyara sashe | gyara masomin]Ana karanta addu'ar istikharan Bayan an idar da sallah, sannan kuma mutum ze iya karanta addu'ar istikharar bayan ya gama karatun tahiya lokacin daya kammala salatul ibrahim kafin ya yiya sallama.
Addu'ar istihara da Larabci
[gyara sashe | gyara masomin]اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ – خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
Rubutun Hausa da harshen larabci
[gyara sashe | gyara masomin]Allahumma innee astakheeruka bi’ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-‘azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata’lamu wala a’lam ,wa-anta ‘allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta’lamu anna hazal-amr (say your need) khayrun lee fee deenee wama’ashee wa’akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta’lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama’ashee wa’aqibati amree fasrifhu ‘annee wasrifnee ‘anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.
Fassara da harshen Hausa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya Allah! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al’amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al’amarina a wata rayuwar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al’amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al’amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al’amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi”.