Jump to content

Jérôme Agyenim Boateng

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jérôme Agyenim Boateng
Rayuwa
Cikakken suna Jérôme Agyenim Boateng
Haihuwa West Berlin (en) Fassara, 3 Satumba 1988 (36 shekaru)
ƙasa Jamus
Ƴan uwa
Ma'aurata Kasia Lenhardt (en) Fassara
Ahali Kevin-Prince Boateng da George Boateng (en) Fassara
Karatu
Harsuna Jamusanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Germany national under-17 association football team (en) Fassara2004-200541
  Germany national under-17 association football team (en) Fassara2005-200541
  Germany national under-19 football team (en) Fassara2005-2007172
  Germany national under-17 association football team (en) Fassara2006-200641
Hertha BSC II (en) Fassara2006-2007241
  Hertha BSC (en) Fassara2007-2007100
  Hamburger SV2007-2010750
  Germany national under-21 football team (en) Fassara2007-2009151
  Germany men's national association football team (en) Fassara2009-2018761
Manchester City F.C.2010-2011160
  FC Bayern Munich2011-ga Yuni, 20212295
Olympique Lyonnais (en) FassaraSatumba 2021-ga Yuni, 2023320
U.S. Salernitana 1919 (en) Fassara2 ga Faburairu, 2024-30 Mayu 202470
  LASK Linz (en) Fassara31 Mayu 2024-
 
Muƙami ko ƙwarewa centre-back (en) Fassara
Mai buga baya
Lamban wasa 17
Nauyi 90 kg
Tsayi 192 cm
Kyaututtuka
IMDb nm3819742
jboateng.com
Jerome Boateng
Jérôme Agyenim Boateng
Jérôme Agyenim Boateng
Jérôme Agyenim Boateng

Jerome Agyenim Boateng (An haifeshi a ukku ga watan satumba 1988), kwararren dan wasan kwallon kafa na kasarJamus wanda yake taka. [1]leda a kungiyar Lask dake a gasar Bundesliga ta kasar Australiya. Boateng ya fara rayuwar kwallonshi a Hartha BSC a inda yasamu cigaba daga matakin masu kananun shekaru zuwa kungiyarsa kwallon kafansa na farko. Bayan yasoma kakarsa ta farko a hertha, yayi gaggawar sa hannu a kungiyar kwallon kafa ta hamsburger sv inda  yashiga acikin mafi muhimmancin yan wasa a kungiyar,wanda ya bada gudummuwa matuka wajen taimaka ma kungiya zuwa mataki na biyun karshe na UEFA EUROPA LEAGUE.

Bayan kammala kakar wasa daya da yayi a ingila, da kungiyar wasan kwallon kafa ta manchester city, yashiga kungiyar wasan kwallon kafa ta bayern munich a shekarar 2011 inda yayi nasarar cin gasoshi na gida dana nahiyar turai,mafi muhimmanci daga ciki shine yayi nasarar lashe ganimomi ukku ajere acikin kakar wasa daya a shekarar 2012-2013 dakuma 2019-2020. Yarjejeniyarsa takare da kungiyar wasan a 30 ga watan yuni na shekarar 2021 inda yazama dan wasan kyauta kafin samun gurbin zama a kungiyar wasan kafa ta lyon. Daga nan kuma, yayi wasa da kungiyar wasa ta salernitana da ke a kasar italiya.

Jerome boateng yayi wasa a jamus acikin yan wasa masu shekaru kasa da shekaru 21 inda yayi nasarar lashe gasar zakarun euro U-21 a shekarar 2009, hakan ya haifar masa da cigaba zuwa matakin dan wasan babban kungiyar kasar. Dan wasan tuni yatara fiye da iyakoki saba'in inda ya wakilci jamus a gasar UEFA Euro 2012,Euro 2016, gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2010,2014 da 2018. Ya kasance daga cikin yan wasa masu matukar muhimmanci wajen jagorantar kasar zuwa ga lashe gasar kofin kwallon kafa ta duniya a shekarar 2014.

Rayuwarsa a matakin kunyoyi

[gyara sashe | gyara masomin]

Rayuwarsa tafarko Boateng yafara rayuwarsa ta kwallon kafa a kungiyar matasa ta Tennis Borussia Berlin, kafin shiga kungiyar Hertha BSC a shekarar 2002.[2]

Hertha BSC Bayan tasowa daga kungiyar matasa,yayi nasarar saka kwallo daya araga acikin wasanni tara a kakar wasa ta 2005-06 [3]yafito a wasanni 15 a kakar wasa ta shekarar 2006-07.[4]Yayi nasarar shiga daga cikin yan wasan farko na tawagar kungiyar a 31 ga watan janairu 2007. Ya halarci karonsu da kungiyar wasan Hannover 96 a filin wasan AWD-Arena,a sati na 19 na kakar wasan 2006-07 na gasar Bundesliga. Ya kasance daga cikin yan wasa nafarko da sukeda tabbacin fitowa a kowane wasa duk kasancewarsa mai karancin shekaru 18. Ya kammala kakar wasansa ta shekarar 2006-07 da wasanni sha daya a kungiyarsa ta farko.[5]


Boateng yasamu hadi inda yayi gaba zuwa kungiyar Hamburger SV a bazarar 2007.[6]Saboda haka,bisa ga kafar sadarwa ta jamus, Boateng bayada ra'ayin saka hannu a kwararriyar yar jejeniya ta shekara biyar da kungiyar Hertha.

  1. edit "FIFA World Cup Russia 2018: List of Players: Germany" (PDF). FIFA. 15 July 2018. p. 12. Archived from the original (PDF) on 11 June 2019.
  2. "Jerome Boateng". kicker.de (in German). Retrieved 28 June 2020.
  3. "Jerome Boateng". kicker.de (in German). Retrieved 24 July 2015.
  4. "Jérôme Boateng » Club matches". World Football. Retrieved 24 July 2015.
  5. "Jérôme Boateng » Club matches". World Football. Retrieved 24 July 2015
  6. " (in German). Abendblatt. 8 July 2007. Archived from the original on 28