Jamhuriyar Musulunci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jamhuriyar Musulunci
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na jamhuriya, Theocracy da Islamic state (en) Fassara
Jamhuriyoyin Islama a kore.

Jamhuriyar Musulunci suna ne da aka ba da nau'ikan gwamnatocin waɗansu ƙasashe. Waɗannan ƙasashe galibi suna da Musulunci a matsayin addinin ƙasa kuma ana gudanar da su da ƙa'idodin Shari'a, dokar musulunci. Dokokin da jihar ta yi ba za su saba wa Shari'a ba.

Waɗannan jihohi suna kiran kansu Jamhuriyar Musulunci (jerin da ba na karewa ba)

  • Iran (bayan an hambarar da Shah Mohammad Reza Pahlavi a 1979)
  • Pakistan (Tun daga tsarin mulki na 1956, aka kafa ƙasar don samarwa da musulmai mazauna kasar Indiya mulkin mallaka, a 1947)
  • Afghanistan (tun lokacin da aka hambarar da Taliban a 2001)
  • Mauritania (tun daga 1958)
  • Sudan
  • Comoros (Jamhuriyar Musulunci ta Tarayyar)
  • Gambiya (tun Disamba 2015)

Duk da irin wannan suna ƙasashen sun banbanta sosai a gwamnatocinsu da dokokinsu.