Janaba
Janaba | ||||
---|---|---|---|---|
Islamic term (en) , Sufi terminology (en) , condition (en) , legal status (en) da social status (en) | ||||
Bayanai | ||||
Ƙaramin ɓangare na | ritual purity (en) | |||
Bangare na | Islamic jurisprudence of worship (en) , Validity of worship in Islam (en) , Corruption of prayer (en) da Corruption of Fasting (en) | |||
Amfani | ritual purity in Islam (en) | |||
Facet of (en) | Najasa (en) , Fasid (en) da batil (en) | |||
Sunan asali | جَنَابَةٌ، اَلْجَنَابَةُ | |||
Vocalized name (en) | جَنَابَةٌ، اَلْجَنَابَةُ | |||
Addini | Musulunci da Sufiyya | |||
Suna saboda | abstinence (en) | |||
Yaren hukuma | Larabci | |||
Al'ada | Islamic culture (en) , Arab culture (en) da cultural globalization (en) | |||
Harshen aiki ko suna | Larabci da multilingualism (en) | |||
Kayan haɗi | Maniyyi | |||
Present in work (en) | Al Kur'ani, Hadisi da Tafsiri | |||
Ta jiki ma'amala da | water in Islam (en) | |||
Alaƙanta da | Ghusl (en) , Alwala da Tayammum (en) | |||
Full work available at URL (en) | corpus.quran.com… da qurananalysis.com… | |||
Wuri | ||||
|
Wankan janaba((الغسل الجنابة)) A Musulunci shi dai wankan Janaba ba kamar sauran wankan da muke yi ba ne na yau da kullun ba, shi yana da ka'idoji da yadda ake yin shi kamar yadda ya zo a littafan addinin Musulunci, kamar su Fiqhu da dai sauran su.
GA YADDA AKE YIN SHI A MUSULUNCI
[gyara sashe | gyara masomin]- 1=>T
- 2=> Sannan zaka sami ruwa mai
tsarki, idan abin da ruwan ya ke a ciki mai budadden baki ne sai a ajiye shi a bangaren hannun dama, idan kuma mai rufaffen baki ne sai a sashi a hannun hagu (kamar buta).
- 3=> Sai a fara da sunan Allah
wato BISMILLAH (amma a zuci, saboda ba a ambaton sunan Allah a yayin da ake cikin bandaki). Sannan a wanke hannu kafin a fara komai sau uku
- 4=> Sannan yana da kyau a sake
yin niyya ace "Nayi niyyar yin wankan janaba, Farilla, domin na gusar da babbar dauda (نويت غسل الجنابة فرض رفع الحدث أكبر)." (ita ma niyyar a zuci. Idan ma ba a fada ba, ba laifi, don niyya tana farawa tun daga sanda aka dauki abin wankan, buta ko bokiti da sauransu).
- => Sannan sai ayi tsarki (da
wankewar gaba da kuma kewayensa). Bayan wannan sai ayi alwala sau ɗaya ɗaya
- => Sai mutum ya hada hannuwansa ya nutsar da su a cikin ruwun wanka, sai ya fito da su ya kakkabe sannan ya shafa kansa gami da murzawa har sau uku zayyi hakan idan ruwan a bokiti ne in kuma a buta ne sai zuba
- Sannan a wanke kai sau
uku, za a shigar har da wuya a wankin kai, da wankin kunnuwa ciki da waje, mace kuma zata zuba ruwa a cikin gashinta ta bubbuga sai ruwan ya shiga ciki sosai. Amma idan tana da larura to anso ta shafa kanta sau ukun ko ina da ina.[1]
- => Sannan a wanke tsagin jiki
na dama tun daga kafada har zuwa kafa, sannan a wanke tsagin jiki na hagu shima tun daga kafada har kafa. a cuccuda sosai da sosai.
- => Sannan sai a game jiki da ruwa duka.
TUNATARWA
[gyara sashe | gyara masomin]Ana so ko ina ya shafi ruwa kamar su matsematsin cinyoyi,da kuma kwarin cibiya duk a tabbatar an cudasu da kyau.Sannan a kula kada a shafi Al'aura don kada alwalar ta karye, (idan ana nufin yin amfani da ita). Domin za'a iyayin Sallah da wannan Alwalar da aka yi wanka da ita, sallah ta inganta.Amma idan bayan wankan aka taba al'aura to sai an sake alwala. Domin shafar farji ko gaba na warware alwalar wanka.
KAMMALAWA
[gyara sashe | gyara masomin]A yi kokari a kiyaye da barin lam'a wato shi ne wani dan karamin wuri a jiki wanda zai zama ruwa bai shafe shi ba, sai a kiyaye. Wankan Janaba ya kammala.
Allah shi ne mafi sani
Kuma Mai tausayin bayinsa
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
An-Nisa UrduScript
-
Quran - year 1874 - Page 27