Jaridar Business Day (Najeriya)
Jaridar Business Day | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | Jaridu na kullun, business newspaper (en) , ma'aikata da classified advertising (en) |
Harshen amfani | Turanci |
Mulki | |
Hedkwata | jahar Legas |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2001 |
Jaridar Business Day, wacce aka kafa a 2001, jaridar kasuwanci ce ta yau da kullun da ke Legas.[1] Ita ce kadai gidan jaridar Najeriya da ke da ofishi a Accra, Ghana[ana buƙatar hujja]. Yana fitar da rahotanni a kullum da kuma ranar Lahadi. Labaranta sun kunshi a Najeriya da Ghana.
Mawallafi
[gyara sashe | gyara masomin]Mawallafin Businessday, shine Frank Aigbogun, tsohon editan jaridar Vanguard.[2][3] Editan jaridar ta yau da kullun shine Tayo Fagbule. Lolade Akinmurele ita ce mataimakiyar editan kuma tana da mataimaka da yawa ita ma. Chuks Oluigbo shine editan yanar gizo yayin da editan taken Lahadi shine Zebulon Agomuo. Jaridar tana da marubuta masu kirkira rubuce-rubuce irin su Iheanyi Nwachukwu, Onyinye Nwachukwu, Jumoke Akiyode, Chuka Uroko, Ifeoma Okeke, Hope Moses Ashike, Olusola Bello, Odinaka Anudu, Obinna Emelike, Teliat Sule, da Chuks Oluigbo, da sauransu.[4]
Jaridar ta fito da ’yan jarida da dama da suka samu lambar yabo. Obodo Ejiro, Teliat Sule da Peter Olowa duk sun banbanta kansu ta hanyar lashe lambar yabo ta Citi Journalistic Award don ƙwarewa a aikin watsa labarai na kuɗi, yayin da Iheanyi Nwachukwu da Patrick Atuanya suka lashe gasar rubutu na Securities and Exchange Commission Capital Market Essay Competition a shekara ta 2012 da kuma 2013 a jere.
Anthony Osae-Brown, tsohon edita, ya kasance ɗan jarida na musamman a lamban yabo na labarai na musamman wato Best Business News Story a cikin watan Mayun 2011, lambar yabo ta Diageo Africa Business Reporting.[5] Godwin Nnanna, wanda tsohon mataimakin editan ne, ya samu lambobin yabo na aikin jarida na duniya da dama da suka hada da lambobin yabo na zinare da azurfa a lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya don bayar da rahotannin jin kai da ci gaba, da lambar yabo na Elizabeth Neuffer Memorial Prize na kafofin yada labarai.[6]
Jaridar ta yi aiki tare da PricewaterhouseCoopers akan bincike na "Girmamawa akan Kamfani da Shugaban Kamfani na Musamman" a shekara ta 2006. Sakamakon binciken ya nuna ra'ayoyin shugabannin Najeriya. An bayar da kyautuka bisa binciken ne a wani biki da aka yi a Legas.[7] A watan Fabrairun 2011, Jaridar Business Day ta shirya taron Babban Kasuwa na shekara-shekara.[8] A watan Maris na 2011 jaridar ta shirya taron kasuwancin ne a ranar SME 2011 a Legas. Taron ya samu halartar 'yan kasuwa, masu ba da shawarwari, masu kudi da wakilai daga masana'antu daban-daban.[9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Nigeria Online News". Columbia University Libraries. Retrieved 13 May 2011.
- ↑ "2006 Awards". Diageo. Retrieved 13 May 2011.
- ↑ "Our tourism heroes, past and present". Daily Sun. 9 February 2008. Archived from the original on 10 August 2011. Retrieved 13 May 2011.
- ↑ "Contact Us". Business Day. Retrieved 13 May 2011.
- ↑ "Diageo Africa Business Reporting Awards 2011 - Finalists Announced". Diageo. 5 May 2011. Retrieved 13 May 2011.
- ↑ "Godwin Nnanna". The Dag Hammarskjöld Scholarship Fund for Journalists. Retrieved 13 May 2011.
- ↑ Craig E. Carroll (2010). Corporate Reputation and the News Media: Agenda-Setting Within Business News Coverage in Developed, Emerging, and Frontier Markets. Taylor & Francis. p. 384. ISBN 978-0-415-87153-2.
- ↑ "Nigerian Bank Nigeria Nigerian Stock Exchange – Foreign Investors Maintain Interest In Nigerian Capital Market". Next (Nigeria). February 2011. Archived from the original on 30 January 2013. Retrieved 13 May 2011.
- ↑ "ConnectNigeria features in Business Day SME Forum 2011". ConnectNigeria. 30 March 2011. Retrieved 13 May 2011