Jibril Isa Diso

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jibril Isa Diso
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 22 ga Afirilu, 1955 (68 shekaru)
Sana'a
Sana'a Malami

Jibril Isa Diso ya kasan ce shine malami kuma makaho na farko a Najeriya daga jihar Kano, masanin ilimi kuma tsohon mai ba gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau shawara [1][2]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Jibril Diso ne a bariki na Gwale karamar hukuma na Jihar Kano . Jibril ya fara karatunsa ne a shekarar 1962 inda kuma ya kammala karatunsa na firamare a shekara ta 1969, ya kuma halarci makarantar sakandaren Gindiri Blinds, jihar Filato tsakanin shekara ta 1979, a shekarar 1984 jami'ar Bayero ta kafa sashen ilimi na musamman saboda Jibril kuma ya karbe shi a matsayin dalibin farko a makarantar. sashen, Jibril ya sami digirin digirgir a fannin ilimi na musamman a Jami'ar London ta Birmingham a shekarar 1991. [3]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Jibril ya fara aikin sa ne a makarantar Tudun Maliki ta mabukata na jihar Kano. Jibril ya shiga sashen ilimi na musamman na jami'ar Bayero ta jihar Kano a shekarar 1994 inda kuma ya zama farfesa na farko da ya fara fuskantar matsalar gani a Najeriya a shekarar 2019. Jibril yana da wallafe-wallafe sama da 10 [4] [5][6][7][8][9][10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Sanusi, Sola (2019-08-27). "Meet Jibrin Isah Diso the first visually impaired professor in Nigeria". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Archived from the original on 2021-05-20. Retrieved 2021-02-25.
  2. "'I want to be the first blind professor in Nigeria'". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2021-02-25.
  3. "PressReader.com - Your favorite newspapers and magazines". www.pressreader.com. Retrieved 2021-02-25.
  4. Meet The First Blind Nigerian Professor Who Was Once A Special Adviser To Governor
  5. Meet The First Blind Nigerian Professor Who Was Once A Special Adviser To Governor
  6. "'I want to be the first blind professor in Nigeria'". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2021-02-25.
  7. "First blind professor: How i defeated disability –Prof Jibrin Diso". The Sun Nigeria (in Turanci). 2019-11-10. Retrieved 2021-02-25.
  8. "Dept of Special Education | Education". edu.buk.edu.ng. Retrieved 2021-02-25.
  9. Ahmed, Ibrahim Ali (2019-08-24). "The Blind Professor". Sen. Ibrahim Shekarau MEDIA (in Turanci). Retrieved 2021-02-25.
  10. Lamai, Samuel (2019-10-31). "Permanent Secretary Presents IVM IKENGA 2020 To Winner Of Raffle Draw". Federal Ministry of Information and Culture (in Turanci). Retrieved 2021-02-25.