Jibril Yakubu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jibril Yakubu
gwamnan jihar Zamfara

7 Oktoba 1996 - Mayu 1999 - Ahmed Sani Yerima
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Jibril Bala Yakubu shi ne mai mulki na farko a jihar Zamfara bayan an kirkire ta daga wani bangare na jihar Sakkwato a watan Oktoba na shekarar 1996, yana rike da mukamin har zuwa lokacin da aka koma kan mulkin dimokaradiyya a watan Mayu na shekarar 1999 a lokacin mulkin soja na Janar Abacha da Abdulsalami Abubakar. A matsayin sa na gwamnan Zamfara, Yakubu ya kirkiri Masarautu guda biyar a jihar tare da sabbin Kansiloli Goma sha daya. Bayan mika shi ga gwamnan farar hula Ahmed Sani Yerima, a watan Mayu shekarar 1999, a matsayin tsohon mai kula da harkokin soja an bukaci ya yi ritaya daga aikin soja.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An kama Yakubu kuma an daure shi bisa zargin da aka gabatar a ranar 9 ga watan Disambar shekarar 1999 wanda ya yi zargin cewa ya hada kai da wasu mutane hudu a shekarar 1996 don kashe Alex Ibru, mawallafin jaridar The Guardian. A matsayinsa na Kwamandan Bataliya ta 29, an yi zargin cewa ya ba da makamai ga 'yan kungiyar da suka kawar da sauran masu adawa da Janar Sani Abacha. A watan Disambar shekarar 2003 alkali ya ki amincewa da bukatarsa ta dakatar da shari’ar. A watan Afrilu na shekarar 2009 kungiyar Arewa Consultative Forum, wata kungiyar masu fafutuka ta Arewa, ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta saki Yakubu Jibril bisa dogaro da manufar sasanta kasa da kwamitin Oputa ya ba da shawarar.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://web.archive.org/web/20051204155350/http://www.thisdayonline.com/archive/2003/10/22/20031022news14.html

http://allafrica.com/stories/201012220252.html