John Michael Ogidi
John Michael Ogidi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 8 Disamba 1959 (65 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Obafemi Awolowo Jami'ar Tsaron Nijeriya Jami'ar Ibadan |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | soja |
Digiri | Janar |
John Michael Ogidi (an haifeshi ranar 8 ga watan disamba, 1959). Tsohon soja ne a Najeriya. Wanda ya riƙe mikamin Manjo Janar [1]. Kuma shine mai bada shawara akan harkar tsaro a kungiyar (High Commission) a ingila (United Kingdom) kafin ritayar sa a watan yuli na shekarar 2015. Shine shugaban (Commander Corps Of Signal Headquarters) a rundunan sojan kasa na Nigeria.
Farkon rayuwa da Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ogidi a ranar 8 ga watan disamban 1959 a Ayibabiri a Jihar Bayelsa na Nigeria.
Yayi makaranta a BDSG a Yenagoa daga shekarar 1973 zuwa 1977. Inda ya samu shaidar gama sakandire. Daganan ya shiga makarnatar soji (Nigerian Defence Academy)[2] a matsayin mamba na 26 a 18 ga watan juni a shekarar 1979 inda ya gama a matsayin mataimakin lutanan (Second Lieutenant) a 18 ga watan disamba 1982. Yana da digiri a inginarin daga Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) Ile Ife da kuma mastas a Jami'ar Ibadan.