Jump to content

John Odey

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
John Odey
Minister of Environment (en) Fassara

17 Disamba 2008 - 29 Mayu 2015
Halima Tayo Alao
Minister of Information and Communications (en) Fassara

26 ga Yuli, 2007 - 17 Disamba 2008
Frank Nweke - Dora Akunyili
Rayuwa
Haihuwa 1 Nuwamba, 1959
ƙasa Najeriya
Mutuwa 7 Oktoba 2018
Karatu
Makaranta Jami'ar Calabar
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

John Ogar Odey (Nuwamba 1, 1959 – 7 Oktoba 2018)[1] an naɗa shi ministan yaɗa labarai da sadarwa na Najeriya a cikin watan Yulin 2007, kuma ya zama ministan muhalli a cikin watan Disambar 2008 bayan shugaba Umaru Yar’Adua ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul.[2][3]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Odey ya kammala karatunsa na B.Sc. a banki da kuɗi daga Jami'ar Calabar a shekarar 1986.[4] Ya kasance mai aiki a kafafen yaɗa labarai, yana da muƙamai kamar babban manajan Sadarwa na Kudu maso Kudu da shugaban Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya.[3] An naɗa shi sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na kasa a cikin shekarar 2004.[4]

Ya yi ministan yaɗa labarai da sadarwa[5] sannan ya zama ministan muhalli a majalisar ministocin Umaru Yar’adua.[6] A watan Maris ɗin shekarar 2010, ya miƙa wa babban sakatare na ma’aikatar muhalli bayan da mataimakin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa.[7]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Odey ya rasu a ranar Lahadi, 7 ga watan Oktoban 2018 a birnin Dubai na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, bayan ya yi fama da ciwon daji[8] wanda ya sa ya fita ƙasar waje neman magani.

Binne[gyara sashe | gyara masomin]

An kai gawar Odey gida a ranar Talata 6 ga watan Nuwamba, 2018, domin a huta a mahaifarsa, Okpoma, ƙaramar hukumar Yala a jihar Cross River, cikin hawaye da shedu. An kai gawar ne da misalin ƙarfe 5 na yamma, kuma an kai gawar zuwa Cocin Christ the King Catholic da ke Okpoma domin gudanar da taro domin karrama shi. An binne shi a Okpoma a ranar Laraba 7 ga watan Nuwamban 2018.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]