Jude Rabo
Jude Rabo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 21 ga Yuni, 1961 (63 shekaru) |
Sana'a |
Jude Rabo (an haifeshi ranar 21 ga watan Yuni, 1961) ɗan Najeriya ne kuma farfesan likitanci a ɓangaren dabobbi, wanda yanzu yake a matsayin mataimakin shugaban Jami'ar Tarayya, Wukari da ke Wukari, a Jahar Taraba a tarayyar Nijeriya.[1][2][3]
Rayuwar farko da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifeshi a tadmu bogoro Jihar Bauchi ranar 21 ga watan Yuni, shekara ta 1962.
Ya fara karatu a makarantar Firamare a tadmun bogoro Jihar Bauchi daga shekarar 1967 zuwa 1975. Ya cigaba da karatun Sakandare a makarantar Gindiri boys secondary school da ke Jihar Plateau, daga shekarar 1975 zuwa 1980. Har-wayau Rabo ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, inda ya karanci fannin likitanci dabobbi daga shekarar 1980 zuwa 1886. Ya wuce Jami'ar Ibadan a shekara ta 1995 zuwa 1999, sannan a Jami'ar Maiduguri inda ya kamala a shekarar 2001, da kuma a International Livestock Research Institute.[1][2][3]
Rayuwar ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Rabo ɗan asalin garin Tadnum ne, Bogoro, Jahar Bauchi. Yana da aure da ‘ya’ya shida.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Aondofa, Chila Andrew (21 January 2021). "Meet Prof Jude Rabo: The New VC Of Federal University Wukari | The Abusites". The Abusites (in Turanci). Retrieved 6 March 2021.
- ↑ 2.0 2.1 "Federal University, Wukari gets new vice chancellor". Premium Times (in Turanci). 2021-01-21. Retrieved 2021-03-06.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 "Federal varsity, Wukari names Jude Rabo as new VC". TheCable (in Turanci). 2021-01-21. Retrieved 2021-03-06.