Jump to content

Kahraba (ɗan ƙwallo)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kahraba (ɗan ƙwallo)
Rayuwa
Haihuwa Kairo, 13 ga Afirilu, 1994 (30 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Egypt national under-17 football team (en) Fassara2011-201161
ENPPI Club (en) Fassara2011-2015369
Egypt Olympic football team (en) Fassara2012-201575
  Egypt national under-20 football team (en) Fassara2012-20122510
  Egypt men's national football team (en) Fassara2013-264
FC Luzern (en) Fassara2013-2014167
  Grasshopper Club Zürich (en) Fassara2014-2014112
Zamalek SC (en) Fassara2015-20195622
Al Ittihad FC (en) Fassara2016-20184420
Clube Desportivo das Aves (en) Fassara2019-201951
Al Ahly SC (en) Fassara2020-3210
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Lamban wasa 7
9
11
11
10
30
7
10
Nauyi 75 kg
Tsayi 182 cm
ezzawi.com…
mohmooud

Mahmoud Abdel Moneim Abdel Hamid Soliman (an haife shi 13 Afrilu 1994) wanda aka fi sani da Mahmoud Kahraba ko kuma ana kiransa da Kahraba, ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Masar wanda ke taka leda a ƙungiyar Al Ahly SC ta Masar da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Masar.[1]

Aikin kulob

[gyara sashe | gyara masomin]

Matasa Kahraba ya fara taka leda a Al Ahly a matsayin matashin dan wasa, inda ya zura kwallaye 36 a wasanni 20 da ya buga a kungiyar yana dan shekara sha biyar bayan ya kulla kawance da Trézéguet. A lokacin yana Al Ahly ne kocin matasa Badr Ragab ya ba shi laƙabi Kahraba ("Electricity") saboda ƙarfinsa da saurinsa. [2][3] Bayan an rufe ƙungiyar matasa a cikin 2011, [4] ya shiga ENPPI kuma ya fara wasansa na ƙwararru a gasar Premier ta Masar a ranar 18 ga Disamba 2011 a wasa da Wadi Degla. Ya zura kwallonsa ta farko a kakar wasa ta gaba yayin wasa da Telephonat Beni Suef bayan da ya zo a madadin.[5] An yi masa tayin gwaji tare da kulob din Hull City na Ingila amma ya kasa tafiya bayan da ya yi fama da neman izinin aiki tare da kocin Hull Steve Bruce yana mai sharhin "dan wasa ne mai matukar kyau, amma shigar da shi kasar cikin dogon lokaci zai zama matsala." [6]