Kel Ahaggar
Appearance
Kel Ahaggar (Berber: ⴾⵍ ⵂⴴⵔ) (trans: "Mutanen Ahaggar") kungiyar Abzinawa ce da ke zaune a tsaunin Hoggar (Dutsen Ahaggar) a cikin Aljeriya. An yi imanin cewa babban magidancin Abzinawa Tin Hinan ne ya kafa kungiyar, wanda kabarinsa yake a Abalessa. Kafuwarta a hukumance tana da kwanan wata kusan dubu daya da dari bakwai da hamsin 1750. An daina aiki da shi tun shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da bakwai 1977, lokacin da gwamnatin Aljeriya ta kawo karshen ta.
Harshen kungiyar shine Tahaggart, yaren Tamahaq.
Kabilu
[gyara sashe | gyara masomin]Kungiyar Kel Aggar ta kunshi kabilu da dama, da suka hada da:[ana buƙatar hujja]
- Iya Loaien
- Dag Rali (kuma an rubuta Dag Ghâli)
- Iregenaten
- Kel Rela, kabilar da ke mulki.
- Kel Silet
- Taituq
- Tégéhé Millet
Shahararrun al'adu
[gyara sashe | gyara masomin]- Wani labari game da kokari a shekarar dubu daya da dari takwas da tamanin da daya 1881 da gwamnatin Faransa ta yi na tuka titin jirgin kasa a tsakiyar sahara, gami da yankin Ahaggar. Tawagar, karkashin jagorancin Laftanar Kanar Paul Flatters, ta kai wa Abzinawa na Kel Aggar hari. [1]
- Fim din a shekarar dubu daya da dari tara da hamsin da bakwai 1957 Legend of the Lost, tare da John Wayne, Rossano Brazzi da Sophie Loren, yana da uku a kan farautar taska a cikin Sahara. Sun ci karo da Kungiyar makiyaya wanda halin Wayne, Joe January, ya ce "Hoggars", kuma ana jin tsoro sosai. [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ball, David W. (1999). Empires of sand . New York: Bantam Books. ISBN 0-553-11014-4 . OCLC 41017491 .
- ↑ Source: the film itself, at around 48 minutes. See also: Legend of the Lost on IMDb