Tin Hinan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tin Hinan
Rayuwa
Haihuwa 4 century
Mutuwa unknown value
Makwanci Abalessa (en) Fassara
Sana'a

Tin Hinan ta kasance sarauniyar tuareg ne a karni na hudu 4, kuma ana bayar da labarun almara akanta, kabarinta mai ban al'ajabi yana cikin Sahara, a Abalessa a cikin Hoggar a yankin Aljeriya .

Sarauniyar Hoggar[gyara sashe | gyara masomin]

Jarumtaka[gyara sashe | gyara masomin]

Wani lokaci ana kiran ta da "Sarauniyar Hoggar" sannan su kuma yan Taureg suna ce mata "Tamenokalt" wanda yake nufin "Sarauniya" Amman kuma a nahawunce yana nufin "mace mai alfarwa", amma kuma ana iya fassara shi da ma'anar kamar "uwar mu dukan mu".

Kabarin Tin Hinan[gyara sashe | gyara masomin]

A farkon karni na 20, an dade da ba da labarin Tin Hinan, kuma mutane da yawa suna tinanin cewa labarine kawai ko kuma almara. Koma yayane, a cikin shekarar 1925, wani mai yawan bude ido ya gano kabarinta, ya kuma tabbatar ta hanyar bada hujjoji cewa, ita din ta rayu a tarihance. ba tada nisa daga zangon Abalessa na Aljeriya, kamar kimanin mil dubu daya 1,000 kwatankwaci kilomita (1550 ) kudu daga babban algeria wato birnin Algiers, a kan wani kwallin dutse , mikakke har kimanin kafa 125 ft kwatan-kwacin (38 mita) a saman mahada biyu na wadis, kabarin yanada sura mai tozo shimfide akan wasu makaman tushe tsawonsu kimanin kafa 88 ft dadai da (mita 27). Ya ƙunshi ɗakuna sha daya ko kuma dakin tattaunawa.

Byron Khun de Prorok ya buɗe kabarin Tin Hinan tare da tallafi daga sojojin Faransa a cikin shekarar 1925, kuma masana ilmin kimiya na dadaddan abu, sun yi zurfin bincike a shekarar 1933. An samu kwarangwa din wata mace, wacce (watakila aka birne a karni na hudu AD) akan wani katako, ta kwantar da bayanta, kanta na kallan gabas. Tana dauke da kayan ado na zinari da kuma wani zinari mau nauyi, wasu daga cikinsu an musu kawa da alamun zane.. A kan tafin hannunta na dama ta sanya mundaye na azurfa 7, a hagunta ma tasanya mundaye na zinare 7. tare da kuma wasu munduwa na azurfa da zoben zinare an sanya su a jikinta an birne, Sannan akwai wani babban sarka na zinari (na gaske da kuma na wucin gadi) suma sun kasance a tare da ita.

An kuma samo abubuwa masu yawa na abubuwan jana'izar ta. Waɗannan abubuwan sun haɗa da mutum-mutumi "Venus" a cikin salon Aurignacian (mai kama da Venus na Hohle Fels ), gilashin kofi (amman ya ɓace a lokacin yakin duniya na biyu), busashshan kahunan zaki , wuƙa wanda aka hada shi da bakin karfe, da kayan adon gwal wanda akayi amfani da fasahan sa akayi kwandalan constantine , aka wallafar a tsakanin 308 da 324 AZ. A ƙarni na 4 zuwa na 5 ya yi daidai da lokacn da'aka ga wani gadonta na katako mai kama da fitilar kantiti na kasar roma wanda sukayi amfani dashi a karni na uku 3, Bayanan Tifinagh an rubuta sune a jikin bangwan dutsi. An gina kabarin ne da irin salan da kowa ya sani a yankin Sahara.

Binciken ilimin halittar mutum wanda aka buga a shekarar 1968 ya yanke cewa kasusuwan tsohuwar mace ce daga cikin zuriyar Rum. Kasusuwan ya nuna cewar watakila bata taba samun haihuwa ba kuma wataƙila ma a sakamakon lalacewar gabobin tane da kuma gurasar ta. A yanzu haka jikin yana cikin gidan kayan tarihi na Bardo da ke Algiers .

Akula[gyara sashe | gyara masomin]

Diddigin bayanai[gyara sashe | gyara masomin]


Bibliography[gyara sashe | gyara masomin]

  • Brett, Michael; Elizabeth Fentress (1997). The Berbers. WileyBlackwell. ISBN 978-0-631-20767-2. Retrieved July 17, 2018.
  • Camps, Gabriel (1974). "L'âge du tombeau de Tin Hinan, ancêtre des Touareg du Hoggar". Zephyrus. 25: 497–516.