Khan na Bollywood

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Khan na Bollywood, sune jarumai maza na masanan'antar finafinan Indiya ta Bollywood wadda take da cibiya a Mumbai. Jaruman sune wadanda sunayen su ya kare da Khan. Daga ciki akwai muhimmai guda uku wato, Shah Rukh Khan da Aamir Khan da Salman Khan Su duka ukun basu da wata dangantaka ta Jini, saidai kuma dukan su suna amfani da Khan a sunayen su kuma dukkan su an haife su ne a shekara daya a 1965 kuma dukkan su Musulmai ne. Su ukun sune mafiya jan hankali a masanan'antar finafinan Bollywood.

Salman Khan
Aamir Khan a 2013
Shahrukh khan
Anass Khan