Jump to content

Shah Rukh Khan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shah Rukh Khan
UNICEF Goodwill Ambassador (en) Fassara

2013 -
Rayuwa
Haihuwa New Delhi, 2 Nuwamba, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Indiya
Mazauni Mumbai
Ƴan uwa
Mahaifi Taj Mohammed Khan
Mahaifiya Lateef Fatima
Abokiyar zama Gauri Khan (mul) Fassara  (25 Oktoba 1991 -
Yara
Ahali Shehnaz Lalarukh Khan (en) Fassara
Karatu
Makaranta National School of Drama (en) Fassara
Jamia Millia Islamia (en) Fassara
Jami'ar Delhi
Sana'a
Sana'a mai gabatarwa a talabijin, jarumi, marubin wasannin kwaykwayo, mai tsara fim, mai rawa, ɗan wasan kwaikwayo, mai tsare-tsaren gidan talabijin da dan wasan kwaikwayon talabijin
Kyaututtuka
Sunan mahaifi Badshah of Bollywood, King of Bollywood da King Khan
Kayan kida murya
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm0451321
Shah Rukh Khan a shekarar 2001
Vidya Balan, Shah Rukh Khan (a tsakkiya) da kuma Priyanka Chopra

Shah Rukh Khan (furuci [ˈʃɑːɦɾʊx xɑːn]; an haife shi a ranar 2 Nuwamban shekarar 1965), kuma ana takaita sunayensa da SRK, Shahararren dan wasan kwaikwayo ne na Indiya wanda ke aiki a masana'antar fim ta Indiya, mai shirya wasanni, kuma fitaccen jarumi. Ana kiransa "Badshah din Bollywood", "Sarkin Bollywood" da kuma "Sarki Khan",[1] Ya fito acikin fina-finai sama da 90, kuma ya samu kyaututtuka da dama, wanda suka hada da 14 Filmfare Awards. Khan nada mabiya da dama a Asiya da mutanen duniya da ba yan'Indiya ba da kuma wadanda asalin su yan'Indiya ne a kasashen duniya baki daya. Dan gane da yawan masu kallon fina-finansa da kudin shiga, An bayyana shi cikin manyan Yan'wasan fina-finan duniya.kuma a sananne a idon duniya ga masu kallon fina finan indiya.

Shah Rukh Khan yafara shirye shiryensa ne da fitowa acikin fina fainan da akeyi a Telebijin a kusan karshen shekara ta 1980s. Yafara fim dinsa na farko a Bollywood a shekarar 1992 acikin fim din Deewana. A Farkon sana'arsa,Shah Rukh Khan ya shaharane da fitowar dayayi a matsayin villainous acikin fim din Darr a shekarar (1993), Baazigar (1993) da Anjaam a shekarar (1994). Daga nan yacigaba da shahararsa bayan yafito acikin wasu jerin wasanni na soyayya (romance), daga cikinsu akwai Dilwale Dulhania Le Jayenge a shekarar (1995), Dil To Pagal Hai a shekarar (1997), Kuch Kuch Hota Hai a shekarar (1998), Mohabbatein a shekarar (2000) da Kabhi Khushi Kabhie Gham... a sheakrar (2001). Ya sami Karbuwa sosai bayan fitowar dayayi a matsayin mai shangiya acikin fina-finan Devdas (2002), fim din NASA na kimyya Swades a shekarar (2004), mai koyar da wasan hockey Chak De! India a shekarar(2007) da mutum mai chiwon Asperger syndrome a fim din My Name Is Khan Wanda yayi a shekarar (2010).

Daga cikin fina-finan sa da suka jamasa cece kuce sune, wani fim na barkwanci na soyayya wato Chennai Express Wanda akayi a shekarar (2013), fim din barkwanci akan fashi Happy New Year (2014), the action film Dilwale (2015), da kuma fim din rigima da cuta Raees (2017). Yawancin fina-finan sa sunfi mayar da hankali ne akan nuna Indian national identity da yadda suke da Alaska data kasashen waje, ko jinsi, launi, da banbancin zamanta kewa dana addini da tausayi da hakuri. Dan taimakonsa da gudunmuwarsa ga wasan fina-finai, Yasa Gwamnatin kasar Indiya ta karrama shi da kyautar Padma Shri, da Gwamnatin kasar Faransa itama tabashi kyautuka biyu dasuka hada da Ordre des Arts et des Lettres da kuma Légion d'honneur.

A shekarar 2015,Shah Rukh Khan nadaga cikin wadannan suka Shugabanci kamfanin motion picture production company Red Chillies Entertainment da Kananan kamfanonin, kuma dashi ne aka mallaki kungiyar wasan Indian Premier League kungiyar cricket Kolkata Knight Riders. Khan mai gudanar da shirye shirye ne a TV da wuraren taruka. Yan'jarida na kiransa da sunan "Brand SRK" saboda karbuwar dayayi a wurare da dama, da kuma masana'antu samarda sana'oin kasuwanci. Ayyukan jinkai da taimakon al'umma da Khan keyi ya taimaka a fannoni da dama kamar kiwon lafiya, da taimakon al'umman da hatsar ko wata bala'i yafara masu, kuma an karrama shi da kyautar UNESCO's Pyramide con Marni award a shekara ta 2011 Dan taimakon sa akan cigaban karatun yara da World Economic Forum's Crystal Award a shekara ta 2018 dan jagorancinsa da kuma nasararsa a wurin kare hakkin mata da yara a kasar Indiya. Kuma Khan yasha fitowa acikin jerin Shahararru kuma jaruman Mutanen Indiya a al'adu Indian culture, a kuma shekara ta 2008 ne, Newsweek tasaka shi cikin jerin mutanen data zaba hamsin masu iko a duniya.

Khan da matarsa Gauri

Sharukhan yanada matar aure guda daya Mai suna ghauri Khan suna da Yara guda biyu namiji daya mace daya.

  1. "Shah Rukh Khan". Forbes (in Turanci). Retrieved 2023-06-18.