Kisan Hanifa Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kisan Hanifa Abubakar
Rayuwa
Haihuwa Nasarawa, 5 ga Afirilu, 2016
ƙasa Najeriya
Mutuwa Nasarawa, 18 Disamba 2021
Yanayin mutuwa kisan kai (child murder (en) Fassara)
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a

Hanifa Abubakar (an haife ta 5 ga wata Afrilu, 2016) ‘yar Najeriya ce da Abdumalik Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids Academy da ke Nassarawa, Jihar Kano, Najeriya, ya yi garkuwa da ita tare da kashe ta.[1] Lamarin dai ya ɗauki hankalin al’ummar kasar saboda karancin shekarun wadda aka kashe da kuma yadda aka kashe ta.

Bayan Fage[gyara sashe | gyara masomin]

Ita kaɗai ce diyar iyayenta, Mista da Mrs. Abubakar.[2][3]

Bacewar ta da kisan nata[gyara sashe | gyara masomin]

Abdulmalik ya sace Hanifa Abubakar ne a ranar 2 ga Disamba, 2021, a wajen makarantar Islamiyya dake dai-dai Kwanar Dakata, Nassarawa, jihar Kano. Ya kai ta gidansa dake Tudun Murtala, karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano. Ya gaya wa matarsa cewa ita ɗiyar ɗaya ce daga cikin ƴaƴan malamansa.[4] A ranar 4 ga Disamba, 2021, ya tuntuɓi danginta kuma ya nemi kuɗin fansa Naira ₦6,000,000.00 ($14,600).[5] A ranar 18 ga Disamba, 2021, Malam Abdulmalik ya gane cewa Hanifa ta gane shi. Bayan ya gama shan shayin da misalin karfe 23:00 na safe, sai ya zuba sauran shayin a cikin wani kwandon da babu kowa a ciki na Bobo Yoghurt (abin sha mai madarar yoghurt ga yara), sannan ya zuba gubar bera a cikin shayin. Tun tana bacci ya ɗauke ta daga gidansa ya shaida wa (matarsa) zai mayar da ita gidan kawunta. Suna cikin tafiya sai ya bawa Hanifa abin sha, ta sha, ya ce mata sai ya ɗauko wani abu (ba'a bayyana sunan abun ba) daga cikin makarantunsu dake Kwanar Yan Gana Tudun Murtala, Nassarawa. Da shigarsu makarantar Hanifa ta rasu. Ya sanya gawar ta cikin buhu ya binne ta a wani kabari mara zurfi tare da taimakon wani Hashim Isyaku.[6]

Abinda bincike ya binciko[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ci gaba da ƙoƙari da tsawaita bin diddigin jami’an ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun kai ga cafke Abdulamalik Tanko, shugaban makarantarta ta Noble Kids Academy da ke Nassarawa a jihar Kano. Mista Tanko ya amsa cewa shi ne ya sace Hanifa kuma ya kashe ta bayan ya lura ta gane shi. Ya haɗa baki da Hashim Isyaku don a binne ta a harabar makarantar. Bayan kama su, Abdulmalik da Hashim sun jagoranci tawagar jami'an ma'aikatar gwamnatin jihar, jami'an 'yan sanda da kuma tawagar likitocin 'yan sanda zuwa ga kabarin. An ciro gawar aka kaita Asibitin kwararru na Mohammed Abdullahi Wase dake Kano, inda aka duba ta sannan aka mika ta ga ’yan uwa domin yi mata jana’iza.

Martani[gyara sashe | gyara masomin]

Mutuwar Hanifa ta ja hankalin kafafen yada labarai a fadin duniya inda maudu'in #JusticeForHanifa (Ayi wa hanifa adalci) ke ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta domin nuna kaɗuwa da bakin cikin faruwar mummunan lamarin. Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya soke lasisin gudanar da duk wasu makarantu masu zaman kansu a jihar, domin tsaftace ayyukan makarantu masu zaman kansu, domin kaucewa sake afkuwar irin wannan lamari a gaba.[7][8] Duk da matakin da gwamnati ta ɗauka na rufe makarantar har abada, ranar 24 ga wata Janairu, 2022, wasu fusatattun matasa da ba a san ko su waye ba, sun mamaye harabar makarantar da tsakar dare suka banka wa makarantar wuta.[9][10]

Gurfana[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 24 ga wata Janairu, 2022, Abdulmalik da sauran wadanda ake zargin Isyaku Hashim da Fatima Jibril an gurfanar da su a gaban kotun majistare da ke Kano. Dukkansu an zarge su da laifin haɗa baki, garkuwa da mutane, boyewa ko tsare wanda aka sace da kuma kisan kai.[11][12]

Hukuncin kisa[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 28 ga wata Yuli, 2022, wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa Abdulmalik da Hashim hukuncin kisa, yayin da aka yanke wa Jibril hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "How Kano girl was abducted and killed by her school teacher". Daily Nigerian. 20 January 2022. Retrieved 29 January 2022.
  2. "Hanifa, our only child, was murdered by a man who should be her protector –Father of five-year-old Kano pupil kidnapped, killed by her school proprietor". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-01-25. Retrieved 2022-09-27.
  3. "Cruel kidnap, murder of Hanifa". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-01-31. Retrieved 2022-07-14.
  4. "How Kano teacher Mohammed kidnapped, murdered 5-year-old Hanifa - P.M. News". Retrieved 29 January 2022.
  5. "Hanifa Abubakar: Nigeria outrage at Kano schoolgirl killing". BBC News. 21 January 2022. Retrieved 29 January 2022.
  6. "Killer proprietor: What I told 5-year-Old Hanifa After Poisoning Her". Daily Trust (in Turanci). 21 January 2022. Retrieved 29 January 2022.
  7. "Hanifa's murder: Kano govt withdraws licences of all private schools". Vanguard News. 25 January 2022. Retrieved 29 January 2022.
  8. "#JusticeForHanifa: Kano shuts school where five-year-old was murdered". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 21 January 2022. Retrieved 29 January 2022.
  9. Mohammed, Bashir (24 January 2022). "Hanifa saga: Irate youth set school on fire". Blueprint Newspapers Limited. Retrieved 29 January 2022.
  10. "Angry Youth set Hanifa Abubakar's school on fire". TVC News. 24 January 2022. Retrieved 29 January 2022.
  11. "Hanifa Abubakar: Kano Arraigns Three Suspected Killers In Court". Channels Television. Retrieved 29 January 2022.
  12. "Hanifa Abubakar: Police arraign suspected killers". Premium Times Nigeria. 24 January 2022. Retrieved 29 January 2022.