Kisan kiyashi a Jihar Kaduna, 2019

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKisan kiyashi a Jihar Kaduna, 2019
Map
 10°20′N 7°45′E / 10.33°N 7.75°E / 10.33; 7.75
Iri aukuwa
crisis (en) Fassara
Kwanan watan 10 –  11 ga Faburairu, 2019
Adadin waɗanda suka rasu 141

A ranar 10-11 ga Fabrairu, 2019, [1] an kashe mutane 141 a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a Najeriya a cewar gwamnan jihar, sa'o'i kaɗan kafin babban zaɓen Najeriya. Waɗanda suka mutu sun haɗa da ‘ yan Adara 11 da Fulani 130. Sai dai an ruwaito ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta fitar da jerin sunayen Fulani 131 da suka mutu sannan ta kuma bayyana cewa an gano gawarwakin Fulani 66 yayin da sauran gawarwakin wasu Fulani 65 suka bace. Wani hari da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton Fulani ne suka kai kan Ungwar Bardi, ya kashe mutane 11 a Adara. Su kuma ‘yan bindigar Adara sun kaiwa Fulani hari.[2][3][4] Daga baya ƙungiyar Miyetti Allah ta bayyana cewa an binne mutane 66 a cikin kaburbura sannan wasu 65 sun bata. [5]

Wasu majiyoyi kamar ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya, sun bayyana cewa gwamnan ya yi karya. Haka ma Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ta musanta hakan.[6] Sai dai an nuna wasu daga cikin kaburburan da aka binne Fulanin da aka kashe a cikin su ga jaridar Premium Times. [7]

Mazauna yankin sun yi ikirarin cewa an fara kai harin ne a matsayin ramuwar gayya a watan Oktoban 2018 tsakanin Kirista da Musulmi a Kajuru wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 55 baki ɗaya.[8] Daga cikin waɗanda suka mutu, 22 yara ne, yayin da wasu 11 kuma mata ne. Rikici a gab da lokutan zaɓe ya zama ruwan dare a Najeriya. An kashe ɗaruruwan mutane a rikicin da ya biyo bayan zaɓen 2011.[9][10][11]

Aƙalla mutane 29 ne aka ruwaito an kashe a wani hari da aka kai a ƙauyen Karamai na Kajuru a ranar 26 ga Fabrairu, 2019. Harin dai ana zargin Fulani ne na matsayin ramuwar gayya ga rikicin da ya ɓarke a baya inda aka kaiwa Fulani hari. Bayan yan kwanaki Gwamnan ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 40.[12][13]

Ƙungiyar haɗin kai akan kashe kashen Kajuru ta bayyana a ranar 18 ga watan Maris cewa tun daga lokacin mutane 130 ne aka kashe a wasu hare-haren ramuwar gayya kan kisan kiyashin da El-Rufai ya sanar.[14]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. SPECIAL REPORT: After attacks, Kajuru villagers tell tales of pains, sorrow
  2. "Death toll from last week's Northwest Nigeria attack doubles to 130". ewn.co.za. Retrieved 2019-02-19.
  3. "Miyetti Allah releases names of 131 victims of Kajuru, Kaduna violence - Premium Times Nigeria".
  4. "'How 66 people were killed in Kaduna in two days'". Premium Times. Retrieved 2019-02-11.
  5. Kajuru Killings: Miyetti Allah Says ‘Adara’ Militia Group’s At Work
  6. El-Rufai lied over killing of 66 Kaduna residents — CAN, NEMA
  7. SPECIAL REPORT: After attacks, Kajuru villagers tell tales of pains, sorrow
  8. Death toll in last week's Nigeria attack doubles to 130
  9. "Gunmen kill 66 in Nigeria's Kaduna state ahead of vote". www.aljazeera.com. Retrieved 2019-02-16.
  10. Nwachukwu, John Owen (2019-02-17). "Kajuru massacre: Fulanis abandon Kaduna village after killing of 66 persons". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2019-02-20.
  11. "Death toll from northwest Nigeria attack doubles to 130". Reuters (in Turanci). 2019-02-19. Retrieved 2019-02-20.
  12. "29 killed as ethnic violence grips NW Nigeria". Archived from the original on 2022-12-19. Retrieved 2022-12-19.
  13. Death Toll From Kaduna Attack Rises To 40
  14. Kajuru killings: Over 130 lives wasted – Group laments