Jump to content

Miyetti Allah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Miyetti Allah
Bayanai
Suna a hukumance
Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria
Mulki
Hedkwata Kaduna
Tarihi
Ƙirƙira 1979
Founded in Kaduna

Ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (a takaice MACBAN ) ƙungiya ce mai fafutukar kare haƙƙin jama'a da ci gaba ko inganta rayuwar Fulani makiyaya a Najeriya.[1] An kafa ƙungiyar ne a farkon shekarun 1970 mai hedikwata a Kaduna. Ta fara aiki bisa doka a cikin 1979 kuma ta sami karɓuwa sosai a matsayin ƙungiyar shawara a cikin 1987.[2]

MACBAN tana wakiltar muradudduka kusan 100,000 masu zaman kansu, na makiyaya a cikin ƙasar.

Suna[gyara sashe | gyara masomin]

Miyetti Allah yana nufin "Na gode wa Allah" a ƴaren Fulfulde.[3]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Takaitattun bayanan tarihin farko na Miyetti Allah ba su da yawa, tarihin baka na wasu mambobin ya samo asali ne tun a shekarun 1960 yayin da wasu kuma zuwa 1972 lokacin da aka kafa ƙungiyar a Kaduna. Mambobin ƙungiyar na farko sun mamaye Fulani ne masu zaman kansu waɗanda tun farkon tunanin Miyetti Allah shine inganta rayuwar su gami da jin daɗin dukkan Fulani ta hanyar taimakon kai.[4] A shekarun 1970, ƙungiyar dake ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Sa’adu ce ke jagorantar ƙungiyar, inda ta kasance mamba a jihohin Kaduna da Filato. Sa’adu wanda haifaffen garin Jos ne amma ya girma a Kaduna, ya kasance jigo a fafutukar neman sabbin mambobi su shiga ƙungiyar.

Jihohin Kaduna da Filato duka suna da rassa na kananan hukumomi da ke da alaƙa da wata karamar hukuma ko al’umma, tarurrukan su ba su saɓawa ka’ida, kuma ba duka wani kudiri ko tsari na ƙasa ko jiha ake bi ba. Amma yayin da ƙungiyar ta faɗaɗa zuwa ƙarin jihohi, manufar ba da fifiko ga ilimin makiyaya da samun damar kiwo daga masu kiwon shanu ya zama jigon gama gari.[ana buƙatar hujja]

Duk da kyakykyawan ƙudiri na ƙungiyar, wasu al’ummar Fulani sun ɗauki Miyetti Allah a matsayin ƙungiyar da ba ta da alaƙa da gwamnati. Hakan ya sa wasu al’ummar Fulani suka yanke ƙauna da Miyetti Allah inda suka kafa nasu kungiyoyin ‘yan banga.[3]

Manufa[gyara sashe | gyara masomin]

Babbar manufa ko burin MACBAN shi ne zama ƙungiyar Fulani makiyaya a cikin ƙasar Najeriya. Ayyukan ƙungiyar sun haɗa da; haɗa kai da gwamnati a madadin gamayyar ƙungiyar makiyaya, haƙƙin amfani da kasa, ilimin makiyaya, uwa uba da magance rikici tsakanin makiyaya da manoma. Har ila yau, ƙungiyar tana goyon bayan samun kariya da kuma ƙara yawan wuraren kiwo ga masu kiwon shanu a ƙasar. Duk da haka, ba duk makiyaya ne ke da niyyar zama wurin kiwo a wuri ɗaya (mamadin yawo) ba, kuma ƙungiyar tana ba da bayanai don shawo kan masu shakkar kiwo tsakanin makiyayan su.[5]

A matsayinsa na babban mai tallata jin daɗin Fulani makiyaya, ƙaruwan rikice-rikicen Samfuri:Verify spelling manoma da makiyaya da satar shanu tun 2011 sun jawo hankalin jama'a da dama aka sansu ga ɗumbin jama'ar da ba su san su ba a baya.

Tsari[gyara sashe | gyara masomin]

Kwamitin amintattu na ƙungiyar na ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi ne kuma tana karɓar kuɗaɗe daga hukumar da sauran masu hannu da shuni. Ana zaɓen shugaban ƙungiyar duk bayan shekaru huɗu. A lokacin da aka kafa MACBAN, ta samu goyon baya daga; Sultan Abubakar III, Aminu Sarkin Zazzau, Usman Nagogo, Sarkin Katsina, da Ado Bayero, marigayi Sarkin Kano. Sarakunan waɗannan masarautun sun haɗa da wani ɓangare na kwamitin amintattu na ƙungiyar.[6]

Haɗakar gamayyar ƙungiyar MACBAN tana da sakatariyar ƙasa a Kaduna da rassa ko ofisoshin a wasu jihohi.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ann, Waters-Bayer; E., Taylor-Powell (1986). "Settlement and land use by Fulani pastorals in case study areas" (in Turanci).
  2. Kuna, Mohammed; Jibrin, Ibrahim. "Rural Banditry and Conflicts in Northern Nigeria" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2021-07-09. Retrieved 2022-12-25.
  3. 3.0 3.1 Blench, Roger. 2016. The fire next time: the upsurge in civil insecurity across the Central Zone of Nigeria. Cambridge: Kay Williamson Educational Foundation.
  4. C., Okali; B., Sule (1981). "The role of pastoralist officials and organizations in solving land use problems" (in Turanci).
  5. "Case study MACBAN". www.enable-nigeria.com. Archived from the original on 2018-11-25. Retrieved 2022-12-25.
  6. "I'm a patron of Miyetti Allah, says Sanusi". TheCable (in Turanci). 2018-01-14. Retrieved 2020-02-07.