Kungiyar Haɗin Kan Dimokuradiyya ta Kasa (Nijeriya)
Kungiyar Haɗin Kan Dimokuradiyya ta Kasa | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | jam'iyyar siyasa |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1994 |
Kungiyar Haɗin Kan Dimokuradiyya ta Kasa wadda gamayyar masu rajin kare dimokaradiyya a Najeriya ne suka kafa ƙungiyar da ake takaita sunan ta da; NADECO, a ranar 15 ga watan Mayun shekara ta1994, waɗanda suka yi kira ga gwamnatin mulkin soja ta Sani Abacha da ta sauka daga mulki domin marawa wanda ya lashe zaɓen 12 ga watan Yunin 1993 MKO Abiola baya.[1] Mambobin ƙungiyar galibi sun fito ne daga kudu maso yammacin ƙasar.[2] Nan da nan suka zama alamar adawa da mulkin soja.[3]
A ranar 11 ga watan Yunin 1994, ta hanyar amfani da ginin da NADECO ta gina, Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa kuma sai ya ɓuya. Fitowar sa keda wuya sai aka kama shi a ranar 23 ga watan Yuni.[4]
Harin bam
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 17 ga watan Nuwamba, 1994, ranar cika shekara ta farko da juyin mulkin Abacha, wani bam ya tashi a filin jirgin saman Legas. A martanin da shugabannin NADECO suka yi, sun yi gargadin "zai zama bala'i, ba wai ga Najeriya kaɗai ba, har ma ga duniya baki ɗaya, idan ƴan Najeriya suka yanke shawarar cewa tashin hankali ne kadai zai sa hankalin ƙasashen duniya ya karkato akan su."[5]
An kama Wale Osun, muƙaddashin sakatare janar na ƙungiyar a ranar 19 ga watan Mayu 1995. Bayan fashewar bam a cikin wannan watan a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ƴan sanda sun kama tare da yi wa Cif Cornelius Adebayo da sauran mambobin NADECO tambayoyi.[6]
Zargi
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin watan Yulin 1997, gwamnati ta zargi ƙungiyar National Democratic Coalition da alhakin kai jerin hare-haren bama-bamai a wuraren da sojoji suka kai hari, kuma ta bayyana a bainar jama'a cewa suna zargin jami'an diflomasiyyar Amurka da sanin tashin bama-baman tun da fari. Sufeto-janar na ƴan sanda, Ibrahim Coomassie, ya ce yana so ya yi wa jakadan Amurka da ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka tambayoyi.[7]
Ƙara
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Agustan shekarar 1999, gamayyar ƙungiyoyin sun shigar da ƙara kan neman diyyar dala miliyan 20, saboda cin zarafin da akai musu a ƙarƙashin gwamnatin Abacha.[8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Nigeria: US Policy". UNIVERSITY OF PENNSYLVANIA - AFRICAN STUDIES CENTER. 12 June 1997. Retrieved 2009-11-26.
- ↑ Eghosa E. Osaghae (1998). Crippled giant: Nigeria since independence. Indiana University Press. p. 294. ISBN 0-253-21197-2.
- ↑ Gilbert M. Khadiagala, Terrence Lyons (2001). African foreign policies: power and process. Lynne Rienner Publishers. p. 30. ISBN 1-55587-966-7.
- ↑ "Background Note: Nigeria". US Department of State. Retrieved 2009-11-26.
- ↑ "CRISIS IN NIGERIA - Call for Oil Embargo". Earth Action. July 1996. Retrieved 2009-11-26.
- ↑ "Africa Denounces Arrests of Human Rights and Pro-Democracy Activists and Continuing Disintegration of Rule of Law". Human Rights Watch. 8 June 1995. Retrieved 2009-11-26.
- ↑ "Nigeria May Ask U.S. Ambassador About Bombings". New York Times. 17 July 1997. p. A9. Retrieved 16 May 2020.
- ↑ "Nigeria: Information on the Persecution of National Democratic Coalition Members in Nigeria". United States Bureau of Citizenship and Immigration Services. 27 October 1999. Retrieved 2009-11-26.