Cornelius Adebayo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cornelius Adebayo
Minister of Transportation (en) Fassara

ga Janairu, 2007 - Mayu 2007
Precious Sekibo (en) Fassara - Diezani Alison-Madueke
Minister of Works and Housing (en) Fassara

Satumba 2006 - ga Janairu, 2007
Obafemi Anibaba - Hassan Muhammed Lawal
Communications minister of Nigeria (en) Fassara

ga Yuli, 2003 - ga Augusta, 2006
Haliru Mohammed Bello - Obafemi Anibaba
gwamnan jihar Kwara

Oktoba 1983 - Disamba 1983
Adamu Atta - Salaudeen Latinwo (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Oke-Onigbin in Isin region, Kwara State (en) Fassara, 24 ga Faburairu, 1941 (83 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
University of Ghana
Kwalejin Barewa
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Malami

Cornelius Olatunji Adebayo tsohon Sanatan kasar Najeriya ne, wanda ya zama gwamnan jiha, sannan ya zama shugaban ma'aikatar sadarwa ta tarayyar Najeriya .

Fage[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Cornelius Olatunji Adebayo ne a ranar 24 ga watan Fabrairu,a shekarar 1941, a Igbaja a Jihar Kwara . Ya yi karatune ar makaranta All Saints Anglican School, Oke-Onigbin, Provincial Secondary School,a jahar Ilorin sannan kuma a Barewa College,dake garin Zaria daga shekarar 1962 har zuwa1963.kuma Ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria (1964-1967), da kuma Jami'ar Ghana, Legon daga (1967-1969). Ya zama malami a jami’ar Ife a shekarar 1969, sannan a shekarar 1973 aka nada shi shugaban sashen turanci a kwalejin fasaha ta jihar Kwara. A tsakanin shekarar 1975 zuwa shekara ta 1978 ya zama kwamishinan ilimi sannan kuma kwamishinan yada labarai da cigaban tattalin arziki a jihar Kwara .

Farkon sana'ar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Kwara a Najeriya

Lokacin da sauye-sauyen da shugaban mulkin soja Laftanar Janar ya kafa. Olusegun Obasanjo ya jagoranci zaben dimokuradiyya a jamhuriya ta biyu a shekarar 1979, an zabi Adebayo a matsayin Sanatan Tarayyar Najeriya mai neman jam'iyyar Unity Party of Nigeria . A shekarar 1983 aka zabe shi gwamnan jihar Kwara, amma ya rasa mukamin a ranar 31 ga Disamba, 1983, lokacin da sojoji karkashin jagorancin Manjo Janar Muhammadu Buhari suka karbe mulki.

Sana'a mai zuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta dubu biyu da bakwai ne [2007], wata kotun birnin Munich ta samu kamfanin Siemens AG da laifin rashin da’a da mu’amalar kwangilar da ba ta dace ba, ta hanyar bayar da cin hanci ga Cornelius Adebayo da sauran su domin samun kwangilar kayayyakin sadarwa. A cewar takardar kotun, an biya tsofaffin ministoci Bello Mohammed, Tajudeen Olarenwaju, Cornelius Adebayo da Alhaji Elewi a matsayin cin hancin dalan kasar amurka miliyan sha bakwai [17] don samun kwangila. A watan Nuwambar shekara ta dubu biyu da bakwai ne [2007] Shugaba Umaru 'Yar'aduwa ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike tare da gurfanar da jami'an da aka ambata a gaban kuliya. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta gayyaci Adebayo domin amsa tambayoyi dangane da hannu a badakalar cin hancin Siemens a lokacin da yake rike da mukamin ministan sadarwa.

manazarta[gyara sashe | gyara masomin]