Jump to content

Kwesi Akwansah Andam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kwesi Akwansah Andam
Rayuwa
Haihuwa 15 Disamba 1946
ƙasa Ghana
Mutuwa 14 Disamba 2007
Ƴan uwa
Abokiyar zama Aba Andam
Karatu
Makaranta Ghana Senior High Technical School (Takoradi) (en) Fassara
Kwame Nkrumah University of Science and Technology
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Malami
Kyaututtuka
Mamba The World Academy of Sciences (en) Fassara

Kwesi Akwansah Andam (15 Disamba 1946 - 14 Disamba 2007) malami ne ɗan ƙasar Ghana kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah.[1] Ya kasance farfesa a fannin Injiniyanci. Ya rasu a ranar 14 ga watan Disamba 2007 a Asibitin Soja na 37.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Farfesa Andam a Ekumfi Atakwaa a tsakiyar ƙasar Ghana a ranar 15 ga watan Disamba 1946.[2] Ya samu takardar shaidar kammala karatunsa a makarantar sakandaren fasaha ta Ghana da ke Takoradi a yankin yammacin Ghana. Ya samu digirin farko na Kimiyya a fannin Injiniyanci a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah. Farfesa Andam ya sami digirin digirgir a fannin Injiniyancin Kwamfuta (CAD) a Jami'ar Newcastle, Newcastle a Tyne a Burtaniya.

A shekarar 1985, an naɗa shi malami a Sashen Injiniyanci na KNUST. Ya zama babban malami a shekarar 1985. Ya zama abokin farfesa a shekarar 1992 kuma cikakken farfesa a shekarar 1997.[1]

Mataimakin Shugaban KNUST

[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa Andam a matsayin mataimakin shugaban jami’ar KNUST ta hukumar gudanarwar jami’ar.[1] Wa'adinsa na shekaru huɗu ya fara a watan Satumba na shekarar 2002 kuma ya ƙare a cikin watan Satumban 2006.[3]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya auri Farfesa Aba Andam wacce masaniya ce a fannin kimiyya kuma malama.[4] Sun haifi 'ya'ya huɗu.[5] Ya rasu a ranar 14 ga watan Disamba 2007 a Asibitin Sojoji na 37 bayan gajeriyar rashin lafiya.[1]

Wallafe-wallafe

[gyara sashe | gyara masomin]

Andam ya rubuta litattafai da takardu sama da 100 na kimiyya.[1]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Prof Kwesi Andam buried". www.modernghana.com. Archived from the original on 12 October 2012. Retrieved 20 July 2011.
  2. "Prof Kwesi Andam buried". www.ghanaweb.com. 30 November 2001. Archived from the original on 22 September 2011. Retrieved 20 July 2011.
  3. "Death of PROF. KWESI A. ANDAM". www2.aau.org. Archived from the original on 4 January 2011. Retrieved 20 July 2011.
  4. "Late Prof. Kwesi Andam Honoured". 5 November 2018. Archived from the original on 7 August 2019. Retrieved 7 August 2019.
  5. "Prof Kwesi Andam buried | General News 2008-03-01". 30 November 2001. Archived from the original on 7 August 2019. Retrieved 7 August 2019.