Langtang, Nijeriya
Langtang, Nijeriya | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Langtang birni ne, kuma ƙaramar hukuma ce a Jihar Filato, Nijeriya. Garin yana a yankin kudancin jihar Filato kuma ya haɗe da; Tunkus, Shendam, Kanam da Wase ta hanyar titi.
Yana da sakatariyar karamar hukuma da fadar Ponzhi Tarok dake tsakiyar garin. Gida ne ga Manyan Janar-Janar na Sojojin Najeriya, waɗanda suka hada da Janar Domkat Bali (marigayi), Joseph Nanven Garba (marigayi), Jeremiah Useni, Joshua Dogonyaro (marigayi), John Shagaya, Jonathan Temlong, Musa Gambo, Yakubu Rimdam, da Ishaku Pennap.. Sauran sun hada da Air Marshal Jonah Wuyep, Air Vice Marshal Napoleon B. Bali, Janar Samuel Nankpak Abashe, Air Commodore Bernard Banfa da kuma Janar Muhammad A. Najib. Gari ne ga dattawan jihohi; Cif Solomon Lar (Gwamnan farar hula na farko a jihar Filato) (marigayi), Cif Ezekiel S. Yusuf (marigayi) (shugaban zartarwa na farko na karamar hukumar Langtang) da Reverend Canon Selchang Miner.
Ilimi da Kiwon Lafiya
[gyara sashe | gyara masomin]Garin Langtang yana da Babban Asibiti da makarantu da suka bazu ko'ina cikin ƙaramar hukumar waɗanda suka haɗa da Kwalejin Mata na Gwamnatin Tarayya, Langtang, Makarantar Sakandaren Gwamnati Langtang. Har-wayau garin na da madatsun ruwa guda biyu da kuma matatar ruwa da don jama'ar garin.
Ƙabila
[gyara sashe | gyara masomin]Babbar ƙabilar garin ita ce Tarok, harshensu shine Tarok, kuma manyan addinan su shine Kiristanci da ATR. Suna samar da amfanin gona kamar gyada, gero, masarar Guinea da sauransu.[1]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Plateau State". Nigeria Direct. Federal Ministry of Information and National Orientation. Archived from the original on 2007-04-18. Retrieved 2007-04-21.