Jump to content

Lauje

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lauje
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na agricultural tool (en) Fassara
Bangare na hammer and sickle (en) Fassara
Amfani harvest (en) Fassara da weed control (en) Fassara
Suna a Kana かま
Lokacin farawa 13 century "BCE"

Lauje wani abu ne da ake ƙerawa da ƙarfe domin yin aikin gona. Akan yi yankan ciyawa dashi domin a baiwa dabbobi na gida, da kuma yankan dawa da gero amma anfi amfani dashi wajen yankan ciyawa wacce ake bawa awakai da tumaki har da dan maraqin sa. Haka kuma Hausawa suna wani karin magana "akwai lauje cikin naɗi"[1] ma'ana in kaji bahaushe yace akwai lauje cikin naɗi, kenan akwai wani munafunci. Ana kuma anfani da kalmar lauje a tatsuniya misali "dadduƙe-dadduƙe har Kano" to idan akayi tatsuniya akace haka sai ka ansa da Lauje an kuma kiranshi da l

lauje, gatari da sauransu, suna daga kayan aikin gona
wannan shine asalin lauje/laushe wanda yake da ɓota ana amfani dashi a ƙasar Hausa a gona da sauransu

Lauje wani abu ne da ake ƙerawa da ƙarfe domin yin aikin gona. Akanyi yankan ciyawa, da kuma yankan dawa da gero amma anfi amfani dashi wajen yankan ciyawa. Haka kuma Hausawa suna wani karin magana "akwai lauje cikin naɗi"[2] ma'ana in kaji bahaushe yace akwai lauje cikin naɗi, kenan akwai wani munafunci. Ana kuma anfani da kalmar lauje a tatsuniya misali "dadduƙe-dadduƙe har Kano" to idan akayi tatsuniya akace haka sai ka ansa da Lauje an kuma kiranshi da laushe.[gyara sashe | gyara masomin]

laujuna da gatari a wata kasuwa a badarawa kaduna

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

Za'a iya gano ci gaban sikelin a Mesopotamiya zuwa lokutan da suka gabata kafin zamanin Neolithic. An tono adadi mai yawa na laushi a wuraren da ke kewaye da Isra'ila waɗanda aka tsara su zuwa zamanin Epipaleolithic (18000-8000 BC). Gudun da aka yi a Wadi Ziqlab, Jordan sun gano nau'o'i daban-daban na katako na farko. Abubuwan tarihi da aka dawo dasu sun kasance daga 10–20 centimetres (3.9–7.9 in)-20 in) a tsawon kuma suna da gefen jagged. Wannan ƙirar 'kamar hakora' mai rikitarwa ta nuna babban ƙira da ƙwarewar masana'antu fiye da yawancin sauran kayan tarihi da aka gano. Sickle blades da aka samu a wannan lokacin an yi su ne da dutse, madaidaiciya kuma an yi amfani da su a cikin motsi na sawing fiye da yadda aka tsara ta zamani. gano raguwa daga waɗannan sikelin a kusa da Mt. Carmel, wanda ke ba da shawarar girbi na hatsi daga yankin kimanin shekaru 10,000 da suka gabata.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-21. Retrieved 2021-06-10.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-21. Retrieved 2021-06-10.