Laura Kutika

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Laura Kutika
Rayuwa
Cikakken suna Laura Guliamo Luyeye Kutika
Haihuwa Kinshasa, 24 ga Augusta, 1984 (39 shekaru)
ƙasa Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Karatu
Makaranta Université de Kinshasa (en) Fassara
Sana'a
Sana'a darakta, marubin wasannin kwaykwayo, marubuci da mai bada umurni na gidan wasan kwaykwayo
IMDb nm13253922

Laura Guliamo Luyeye Kutika (an haife ta a ranar 24 ga watan Agustan shekara ta 1984) ita ce darektan fina-finai kuma marubuciya a ƙasar Kongo.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Kutika a Kinshasa, Zaire. Daga shekarun 2001 zuwa 2003 ta kasance co-writer a jerin shirye-shiryen talabijin na Kinshasa Hôtel.[1] Ta sami digiri na farko a fannin wallafe-wallafen kuma ta yi karatun shari'a a Jami'ar Kinshasa. Kafin ta kammala karatunta, Kutika ta yanke shawarar bin sha'awarta ga rubuce-rubuce kuma ta ɗauki horo a talabijin da rubuce-wallace na rediyo. A shekara ta 2002, ta kasance co-writer na wasan kwaikwayo na rediyo, Cibiyar Lokole ta Kinshasa.[2] Kutika ta koma Faransa a shekara ta 2003 don yin aiki a matsayin darekta.[1]

A shekara ta 2009, Kutika ta kasance mataimakiyar darektan gajerun fim ɗin Entre chat et chien na Barbara Barbet. Kutika ta ba da umarnin gajeren fim ɗin Vas-y fonce a watan Mayu 2011.[2] A shekara ta 2012, ta rubuta littafinta na farko, Seule, face au destin. Kutika jagoranci Moumoune et moi a cikin shekarar 2013. Littafinta na biyu, À nos actes manqués, an wallafa shi a shekarar 2014. A shekara ta 2015, ta jagoranci fim ɗin Abeti Masikini: Le Combat d'Une Femme tare da Ne Kunda Nlaba. Fim ɗin girmamawa ga mawaƙa Abeti Masikini kuma yana nazarin rayuwarta da tasirin ta. Tunanin fim ɗin ya zo ne bayan Kutika ta karanta tarihin Masikani na Berthrand Nguyen Matoko, wanda ya shawarce ta game da yin fim ɗin.[3] Ta sami kyautar mafi kyawun shirin a bikin Cinema Au Feminin a Kinshasa.[4]

Kutika mahaifiyar yara uku ce. Tana yin taekwondo. Kutika ita shugabar kungiyar agaji ce ta "Le nouveau rire".[5]

Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]

  • 2001-2003: Kinshasa Hôtel (writer)
  • 2009: Entre chat et chien (assistant director)
  • 2011: Vas-y fonce (director)
  • 2012: Ndouleman (assistant director)
  • 2013: Moumoune et moi (director)
  • 2015: Abeti Masikini: Le Combat d'Une Femme (writer/producer/director)

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "[Afrique/Congo-Brazzaville/RDCongo] Film documentaire : Laura Kutika immortalise la diva Abeti Masikini". Media Part (in French). 20 February 2014. Retrieved 19 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  2. 2.0 2.1 "Laura Kutika". Culture Congo (in French). 3 February 2016. Retrieved 19 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  3. Cana, Franck (20 February 2014). "Film documentaire : Laura Kutika immortalise la diva Abeti Masikini". Pages Afrik (in French). Archived from the original on 7 December 2020. Retrieved 19 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  4. "LE FILM ABETI MASIKINI: LE COMBAT D'UNE FEMME A REMPORTE LE PRIX DU MEILLEUR DOCUMENTAIRE AU CINEF 2018". Skyrock (in French). 17 July 2018. Archived from the original on 28 November 2020. Retrieved 19 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  5. Taino, Ferdinand (19 February 2014). "Film documentaire : Laura Kutika immortalise la diva Abeti Masikini". Alwihda Info (in French). Retrieved 19 November 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)