Lawal Sama'ila
Lawal Sama'ila Yakawada tsohon ciyaman ne a garin giwa karamar hukumar Giwa, Jihar Kaduna. Kuma tsohon sakataren[1] gwamnatin Jihar Kaduna ne[2]
A lokacin marigayi gwamna Patrick Ibrahim Yakowa. Lawal Yana daga cikin wadanda ake damawa dasu a [3]siyasar gwamnatin jihar kaduna.[4][5][6][7]sannan shine me bama gwamnan jihar shawara a lokacin tsohon gwamnan Malam Nasir Ahmad elrufa I
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Lawal ya koyi siyasa ne tun a gida gurin mahaifin sa kasancewar sa Yana mulkar Al,umma. lawal ya zauna tare dashi , sannan ya zauna da mutane da dama inda ya koyi siyasar mutunta mutane da kawo musu cigaba , lawal ya fara zama shugaban Al,umma tun a lokacin da yake karatu a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, lawal yayi shugabancin karamar hukumar Giwa, Kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Kaduna.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Lawal yayi karatun sa na muhammadiyya a garin su yakawada Karamar hukumar giwa, yayi firamare acan daga Nan yazo kwalejin Sardauna dake Zaria daga Nan ya shiga jami'ar Ahmadu bello Dake Zaria.
Aure
[gyara sashe | gyara masomin]Lawal Yana da mata guda biyu hassana wacce itace uwargida, Sai amarya asma,u, suna da Yara da dama dashi.yana da manyan yara.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://dailytrust.com/new-boards-of-parastatals-inaugurated/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/tag/lawal-samaila-yakawada
- ↑ https://dailynigerian.com/kaduna-apc-welcomes/
- ↑ https://hausa.legit.ng/1181149-lawal-samaila-yakawada-da-uba-sani-na-neman-zama-sanata-a-kaduna.html
- ↑ https://thenationonlineng.net/tag/ssg/page/7/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-17. Retrieved 2023-07-17.
- ↑ https://guardian.ng/news/kaduna-govt-sets-up-65-man-transition-committee-for-may-29-handover/