Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya (Najeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya (Najeriya)

Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya ta kasance daya daga cikin Ma’aikatun Tarayyar Najeriya da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya . Ministan jiragen sama na yanzu shi ne Hadi Sirika . Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi ne a ranar 21 ga watan Agusta shekarata 2019. [1]

Ƙungiya[gyara sashe | gyara masomin]

Ma’aikatar ita ce ke da alhakin tsarawa da kuma kula da manufofin gwamnati na jiragen sama a Najeriya.

Kai tsaye take da alhakin kula da sufurin jiragen sama, cigaban tashar jiragen sama da kuma kiyayewa, samar da ayyukan more rayuwa da sauran buƙatun rayuwa. Ma’aikatar tana karkashin jagorancin Ministan da Shugaban kasa ya naɗa, tare da taimakon Babban Sakatare, wanda ma’aikacin gwamnati ne. Ma’aikatar ita ce ke da alhakin kula da wadansu bangarori kamar su Kwalejin Fasahar Jirgin Sama na Najeriya . Ma’aikatar na da hedikwata a Abuja . [2] A baya babban ofishin yana Legas.[3]

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya[gyara sashe | gyara masomin]

Sirika Hadi tsohon matuƙin jirgin sama ne, Tsohon Janar Manajan Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Katsina, tsohon dan Majalisar wakilai ta Tarayya, kuma Sanata a Tarayyar Najeriya, wanda ke wakiltar gundumar Sanata ta Katsina ta Arewa a ƙarƙashin ƙungiyar Congress for Progressive Change. Sirika ya riƙe mukamin (Mataimakin Shugaban) Kwamitin cigaban muradun ƙarni (MGDs) wanda Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa . Ya zama Sanata a 2011. Yanzu haka shi ne Ministan Sufurin Jiragen Sama na Tarayyar Najeriya.

Sassan[gyara sashe | gyara masomin]

A baya Sashen Kula da Sufurin Jiragen sama na ma'aikatar ya binciki hatsarin jirgin sama. A cikin 1989 Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya (FCAA) ta bude, kuma Sashen Kula da Sufurin Jiragen Sama ya zama Sashen Kula da Tsaro na FCAA. A cikin wannan shekarar aka kafa Ofishin Binciken Hatsari (AIB), wanda ke ƙarƙashin Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama, kuma FCAA ba ta da sauran alhakin binciken haɗari. Daga baya aka canza sunan ofishin zuwa Ofishin Bincike da Rigakafin Hatsari. A zaman wani bangare na dokar sufurin jiragen sama ta shekarar 2006, AIB ta zama hukuma mai cin gashin kanta, Ofishin Binciken Hadarin . [4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. http://aviation.gov.ng
  2. "LIST AND ADDRESSES OF FEDERAL MINISTRIES IN NIGERIA." Embassy of Nigeria, Washington, D.C. Retrieved on 8 September 2010. "FEDERAL MINISTRY OF AVIATION Fed. Secretariat, Shehu Shagari Way Abuja"
  3. "CIVIL AIRCRAFT ACCIDENT REPORT NO. CIA 129 Archived 2012-06-17 at the Wayback Machine." () Federal Ministry of Aviation. Retrieved on 7 June 2012. "Federal Ministry of Aviation, Joseph Street, Lagos"
  4. http://www.xtremeloaded.com/2268/list-of-current-nigerian-ministers-2015-updated/ Archived 2017-07-25 at the Wayback Machine Full list of Nigerian ministers from 2014-2015