Mahathir Mohamad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Mahathir Mohamad
Malaysian Prime Minister Mahathir Mohamad (42910851015) (cropped).jpg
ɗan Adam
jinsinamiji Gyara
ƙasar asaliMaleziya Gyara
sunan asaliMahathir bin Mohamad Gyara
sunan haihuwaMahathir bin Mohamad Gyara
pseudonymTun M, Dr M Gyara
lokacin haihuwa10 ga Yuli, 1925 Gyara
wurin haihuwaAlor Setar Gyara
mata/mijiSiti Hasmah Mohamad Ali Gyara
yarinya/yaroMarina Mahathir, Mokhzani Mahathir, Mukhriz Mahathir Gyara
harsunaMalaysian, Turanci Gyara
sana'aɗan siyasa, likita, marubuci Gyara
muƙamin da ya riƙePrime Minister of Malaysia Gyara
makarantaUniversity of Malaya Gyara
academic degreedoctorate Gyara
honorific suffixRoyal Family Order of Kedah Gyara
jam'iyyaUnited Malays National Organisation, Malaysian United Indigenous Party Gyara
addiniSunni Islam Gyara
official websitehttp://chedet.cc/ Gyara
patronym or matronym for this personMohamad Gyara

Mahathir bin Mohamad Kalmar|Jawi: محضير بن محمد; IPA: IPA-may|maˈhaðɪr bɪn moˈhamad|; An haife shi a 10 ga watan yulin shekara ta 1925)[1] dan siyasar kasar Malasiya ne kuma firayim minista maici ayanzu karo nabiyu. Shine Shugaban gamayyar Pakatan Harapan,[2] kuma danmajalisar kasar, dake wakiltar mazabar tarayya ta Langkawi dake Kedah. Kafin nan yarike firayim minista daga 1981 zuwa 2003, inda yazama wanda yafi dadewa a karagar. Siyasar Mahathir tafi tsawon shekara saba'in (70) tun bayan shigarsa sabuwar jam'iyar United Malays National Organisation (UMNO) a shekarar 1946; ya kirkira jam'iyar Kansa wato Parti Pribumi Bersatu Malaysia (Malaysian United Indigenous Party), a shekara ta 2016.[3][4]

An haife shi da girmarsa a Alor Setar, Kedah, Mahathir yakasance maikwazo a makaranta haka yasa yazama likita. Yazama jigo a cikin jam'iyar UMNO kafin yaje Majalisa 1964. Yayi tenure daya ne kawai, sai yakasa cin kujerarsa kuma yayi rashin nasara ne da firayim ministan waccan lokaci wato Tunku Abdul Rahman[5] kuma an koreshi daga jam'iyar UMNO. Yayin da Abdul Rahman yayi marabus, Mahathir yasake shiga UMNO da zuwa Majalisa, kuma Karin girma zuwa fadar gwamnati, a 1976 yakai matsayin mataimakin firayim minista, kuma a 1981 aka rantsar dashi a matsayin firayim minista bayan ubangidansa yayi marabus, Hussein Onn.

A lokacin mulkin Mahathir a matsayin firayim minista na farko, kasar Malaysia tasamu cigaban zamani da farfadowar tattalin arziki, kuma gwamnati ta fara kafa ayyukan gine-gine. Mahathir yakasance Shugaban daya jima a mulki, yayi nasara harsau biyar a babban zaben Kasar, samun karfinsa yafaru sanadiyar cin gashin kanta da akaba hukumar Shari'ar kasar da kuma karfin masarautar kasar Malaysia. Ya kawo dokar da aketa cecekuce akai ta kulle masu sukar gwamnati wato Internal Security Act da kuma masu bin kananan addinai da abokanan hamayyar siyasa harda mataimakin firayim ministan daya kora a 1998, Anwar Ibrahim. Mahathir yayi fice a kin bayarda yancin mutanen sa, da kuma kiyayyarsa akan bukatun kasashen yamma da tsarin tattalin arziki yasa alakarsa da Kasar Amurika da United Kingdom da kuma Australia, da wasunsu tayi tsami. A matsayin sa na firayim minista ya rika rajin cigaban kasashen da basu da karfin tattalin arziki da duniya bakidaya.

Bayan yanar mulki, Mahathir yazama mai sukan Shugaban daya zaba da hannunsa yagaje shi Abdullah Ahmad Badawi a 2006, da kuma Najib Razak a 2015.[6] dansa Mukhriz Mahathir shine Chief Minister dake Kedah har zuwa farkon shekara ta 2016. A 29 ga watan February 2016, Mahathir yafita daga jam'iyar UMNO dalilin goyon bayan firayim minista Najib Razak, dukda 1Malaysia Development Berhad scandal.[7] A 9 September 2016, yayi wa jam'iyar sa Malaysian United Indigenous Party rijista a matsayin jam'iyar siyasa, kuma shine Shugaban ta.[8] A 8 January 2018, Mahathir yazama Dan takarar jam'iyar gamayyar Pakatan Harapan danyin takarar firayim ministan Malaysia a babban zaben 2018, a wani shirin yafewa Anwar Ibrahim da kuma iya bashi mukami idan ansamu nasara.

Bayan samun nasarar jam'iyar Pakatan Harapan a zaben 2018, An rantsar da firayim minista Mahathir a 10 May 2018. Yana da shekaru 98, shine tsohon Shugaban kasa maici a duniya.[9] shine firayim minista dabai wakiltar YAN jam'iyar gamayyar Barisan Nasional ko wanda tagabace ta Alliance Party kuma mutum na farko da yayi mulki Katsina jam'iya biyu daban daban kuma ba'a Jere ba.

Madogara[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. cite web|url=https://books.google.com/books?id=QiP2DAAAQBAJ&pg=PT8&dq=Mahathir+Mohamad+10+july&hl=en&sa=X&ved=0ahUKEwjct8DSxJvUAhVH1iwKHeaYD7cQ6AEILDAD#v=onepage&q=Mahathir+Mohamad+10+july&f=false%7Ctitle=MALAYSIA POST-MAHATHIR: A Decade of Change|first1=Professor James|last1=Chin|first2=Professor Joern|last2=Dosch|date=15 August 2015|publisher=Marshall Cavendish International Asia Pte Ltd|via=Google Books
  2. cite news|url=https://www.straitstimes.com/asia/se-asia/mahathir-named-chairman-anwar-named-de-facto-leader-of-pakatan-rakyat%7Ctitle=Mahathir named chairman, Anwar named de facto leader of Pakatan Harapan
  3. cite news|url=https://www.reuters.com/article/us-malaysia-mahathir-idUSKLR14546620080519%7Ctitle=Malaysia's PM in danger as Mahathir quits party
  4. cite news|url=https://www.straitstimes.com/asia/se-asia/mahathir-quits-umno-calling-it-najibs-party%7Ctitle=Mahathir quits Umno, calling it 'Najib's party'
  5. cite book|last1=Abdul Rahman|first1=Tunku|title=May 13 – Before and After|date=September 1969|publisher=Penerbitan Utusan Melayu|location=Kuala Lumpur|pages=117–121
  6. Kaos Jr., Joseph (4 April 2015). "Dr M past his quiet stage, asks Najib to step down". The Star (Malaysia). Retrieved 7 August 2015. 
  7. cite news|url=http://www.thestar.com.my/news/nation/2016/02/29/dr-mahathir-quits-umno-again/%7Ctitle=Dr Mahathir quits Umno, again |date=19 February 2016|work=The Star Online|accessdate=15 October 2016
  8. cite news|url=http://www.freemalaysiatoday.com/category/nation/2016/09/09/dr-mahathirs-new-party-officially-registered/%7Ctitle=Dr Mahathir's new party officially registered |date=9 September 2016|work=Free Malaysia Today FMT News|accessdate=15 October 2016
  9. cite news|url=https://www.cnn.com/2018/05/10/asia/malaysia-election-mahathir-victory-intl/index.html%7Ctitle=Malaysia's Mahathir Mohamad is now the world's oldest leader|last=CNN|first=Euan McKirdy, Marc Lourdes and Ushar Daniele,|date=|work=CNN|access-date=11 May 2018