Mahuta
|
| ||||
| Wuri | ||||
| ||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
| Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
| Birni | Katsina | |||


Mahuta dai gari ne mai matukar tasiri da yawan al'umma A cikin karamar hukumar Dandume a jihar Katsina. Garin Mahuta gari ne dake gabashin garin Dandume wadda ita ce hedikwatar qaramar hukumar dandume. Mahuta na da mazabu ward wato Mazabu guda uku (3), Mahuta(A) Mahuta(B) da kuma Mahuta(C) Garin mahuta shi ne gari mafi girma a karamar hukumar bayan cikin garin Dandume An qirqiri garin na mahuta a shekara ta alif da dari tara da tara (1909).
Mutanen garin Mahuta suna noma, kiwo da kuma kasuwanci dai dai gwargwadon iko. Bugu da kari Kuma mutanen na garin Mahuta suna kokari wajen neman ilimi musamman na boko da na addinin Musulunci, kuma Allah madaukakin sarki ya albarkaci 'ya'yansu da basirar fahimtar karatu. Bangaren karatun addini ma ba'a barsu abaya ba, kuma akwai makarantun allo wadanda basa kirguwa, banda zaurukan karatuttuka da masallatai, akwai islamiyoyi da dama na bangaren izala da kuma darika. Bangaren karatun zamani ma ba'a barsu a baya ba inda suke da firamare har guda biyar (5), ga kuma sakandire babba da karama. Akwai 'yan secondary, masu N.C.E, Diploma, Degree, Masters, PhD har da ma Farfesa duk a cikin garin Mahuta. A yanzu haka, Shugaban karamar hukumar Dandume, Alhaji Bashir Gyazama dan asalin garin Gyazama ne, wadda a karkashin mazabar Mahuta (A) take, Dan majaliar jaha Mai wakiltar karamar hukumar Dandume Alh. Yahaiya Nuhu Mahuta shima Dan Mahuta ne. Vice Chancellor na Jami'ar Umaru Musa Yar'adua dake Katsina Farfesa Shehu S.S Muhammad Dan Mahuta ne.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Garin mahuta dai dadadden gari ne da ya samo asali sama da shekara casa'in (90), kuma a wancan lokacin garin ya shahara wajen kasuwanci a yankin, inda garin ke da babbar kasuwar da take tasiri a yankin gaba daya tare da hamshakan manoma a cikin garin dama yankin baki daya.
