Malado Kaba
Malado Kaba | |||
---|---|---|---|
4 ga Janairu, 2016 - 26 Mayu 2018 ← Mohamed Diaré (en) - Mamadi Camara (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Monrovia, 22 ga Maris, 1971 (53 shekaru) | ||
ƙasa | Gine | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Paris (en) | ||
Harsuna | Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Mai tattala arziki | ||
Mahalarcin
|
Malado Kaba (an Haife shi 22 Maris 1971) kwararriya ce kuma masaniyar tattalin arziƙin Guinea kuma mace ta farko Ministar Tattalin Arziƙi da Kuɗi ta Guinea. Ta yi aiki daga watan Janairu 2016 har zuwa watan Mayu 2018.[1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Malado Kaba a ranar 22 ga watan Maris 1971 a Montserrado County, Monrovia, Laberiya. Ita da iyayenta sun ƙaura zuwa Faransa lokacin tana 'yar watanni 3.
Ta yi amfani da yarinta da shekarunta a tsakanin Paris da kewaye. Kaba ta halarci Lycée Honoré de Balzac a Paris inda ta sami baccalauréat a shekarar 1989.[2][3] Ta kammala karatu daga Jami'ar Paris Nanterre a shekara ta 1994 tare da digiri a fannin tattalin arziki da ci gaba da digiri a fannin tattalin arziki na duniya a shekarar 1994.[4] Har ila yau, tana da takaddun shaida daga Cibiyar Goethe a matsayin kwararriya mai amfani da harshen Jamusanci.
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Kaba ta yi horo a ma'aikatar harkokin wajen Faransa[5] kafin ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara a ma'aikatar tattalin arziki da kuɗi ta Guinea daga shekarun 1996 har zuwa 1999. Ta yi aiki kan ayyukan raya ƙasa da dama tare da Tarayyar Turai tare da kula da nazarin dangantakar da hukumar Tarayyar Turai ke yi da Afirka ta Kudu mai alaka da macroeconomics da fayyace kasafin Kuɗi.
A cikin shekarar 2014, Kaba ta zama shugaban shirin Mulkin Afirka na tsohon Firayim Ministan Burtaniya Tony Blair.
Shugaba Alpha Condé ya naɗa Kaba a matsayin ministar kudi a ranar 6 ga watan Janairun 2016, mace ta farko a wannan matsayi kuma ɗaya daga cikin mata bakwai da aka naɗa a majalisar ministoci.[4][6]
A cikin shekarar 2020, an zaɓi Malado Kaba don shiga cikin "aji na farko na Shugabannin Amujae, aji na 2020" na Cibiyar Shugabancin Mata da Ci gaban Ellen Johnson Sirleaf, wanda Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kafa. Manufar shirin Amujae shine canza yanayin mata a cikin jagorancin jama'a a Afirka.[4][7][8]
A watan Mayun 2022, an naɗa Malado Kaba Darakta a Sashen Jinsi, Mata da Jama'a na Bankin Raya Afirka (AfDB). Naɗin da aka yi mata ya fara aiki ne daga ranar 16 ga watan Yuni, 2022.[9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "L'Historique du ministère de l'Economie et des Finances de Guinée". mef.gov.gn. Archived from the original on 2023-04-11. Retrieved 2023-12-10. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "Malada Kaba" (in French). Leaders Afrique. 8 December 2016.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ Freland, François-Xavier (8 March 2017). "Guinée : pour Malado Kaba, ministre de l'Économie, " on peut s'endetter quand il s'agit d'investir dans des projets productifs "". Jeune Afrique (in French). Retrieved 16 May 2017.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ 4.0 4.1 4.2 Tagba, Kamailoudini (7 January 2016). "Guinea: Malado Kaba, country's new Minister of Economy & Finance". The North Africa Post. Retrieved 16 May 2017.
- ↑ Diallo, Malick (11 January 2016). "Guinea: Malado Kaba, New Minister of Economy". Africa News Agency. Archived from the original on 18 October 2018. Retrieved 16 May 2017. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "Commodities, Rainfall, Instability Biggest Challenges —African Ministers". International Monetary Fund. 8 October 2016. Retrieved 16 May 2017.
- ↑ "Commodities, Rainfall, Instability Biggest Challenges —African Ministers". International Monetary Fund. 8 October 2016. Retrieved 16 May 2017.
- ↑ "Malado Kaba | Amujae Initiative". EJS Center (in Turanci). Archived from the original on 2020-06-16. Retrieved 2020-06-16. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "La guinéenne Malado Kaba à la tête du département genre de la Banque Africaine de Développement (BAD)". Financial Afrik (in Faransanci). Retrieved 2022-05-21.