Marina Yannakoudakis

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Marina Yannakoudakis
member of the European Parliament (en) Fassara

14 ga Yuli, 2009 - 30 ga Yuni, 2014
District: London (en) Fassara
Election: 2009 European Parliament election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Paddington (en) Fassara, 16 ga Afirilu, 1956 (67 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Makaranta Brunel University London (en) Fassara
The Open University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Wurin aiki Strasbourg da City of Brussels (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Conservative Party (en) Fassara
marinayannakoudakis.com

Marina Yannakoudakis (an haife ta a ranar 16 ga watan Afrilu, shekara ta 1956) memba ce ta Kwamitin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Turai kuma tsohuwar memba ce karkashin jam'iyyar Conservative na Majalisar Turai a kasar London. An zabe ta a zaben Majalisar Turai a shekarar 2009. Ta rasa kujerar ta a zaben shekara ta 2014.

Kuruciya[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Yannakoudakis a Paddington. Ta yi karatuttukan ta tun daga matakin digirin ta na farko dana biyu a fannin ilimin gwamnati, siyasa da tarihin zamani daga Jami'ar Brunel, inda ta kasance shugabar dalibai na jam'iyyar Conservative, sannan ta sami digiri na biyu a fannin ilimi koyarwa daga Open University.

Ta kasance memba na Majalisar Barnet London Borough Council daga mazabar Oakleigh Park Ward tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2010 inda ta kasance shugaban Kwamitin Tsabta wato Cleaner, Greener, Transport and Development Overview & Scrutiny Committee.

'Yar Majalisar Tarayyar Turai[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kasance cikakkiyar memba na kwamitin kare hakkin mata da adalci tsakanin jinsi, Kwamitin Muhalli, Kiwon Lafiyar Jama'a da Tsaron Abinci da kuma mamba a madadin Kwamitin Musamman kan Laifukan da aka Shirya, Cin Hanci da juya haramtacciyar kudi da Rashawa. Ta kasance memba a Kwamitin Haɗin gwiwar Majalisar Tarayyar Turai da Jamhuriyar Yugoslavia ta Macedonia.[1]

Ta kuma kasance mamba a kungiyar tuntubar manyan jami'an hulda da jama'ar <a href="./Turkish%20Cypriot" rel="mw:WikiLink" title="Turkish Cypriot" class="mw-redirect cx-link" data-linkid="100">Turkish Cypriot</a> da ke arewacin tsibirin, kuma ta kasance mai magana da yawun jam'iyyar Conservative da kuma Turai da masu neman sauyi kan hakkin mata da adalci tsakanin jinsi.

Hakkin Mata[gyara sashe | gyara masomin]

Yannakoudakis ta yi kamfe na nuna adawa da shirin EU na bai wa mata hutun makonni 20 da cikakken albashi. Ta jagoranci kiraye-kirayen kwamitin kare hakkin mata da daidaiton jinsi don tantance tasirin dokar da za a gudanar wanda ya sa aka yi watsi da shawarwarin.[2] Ta kuma tofa albarkacin bakinta kan kudirinta EU na samar da sashi ga mata a dakunan kwana, inda ta bayyana shawarwarin a matsayin "siyayya". >[3]

Ta matsa kaimi wajen yin gyara ga shari'ar Test Achats vs Council of Ministers, hukuncin Kotun Turai wanda ta yanke hukuncin cewa ba ya bisa ka'ida ga kamfanonin inshora su nuna wariya dangane da jinsi a Tarayyar Turai.[4]

Yannakoudakis ta kuma yi ayyuka kan lamuran da suka shafi mata da harkokin kasuwanci[5] da kuma kare hakkin yara.[6]

Yannakoudakis ta jagoranci kamfe don yaki da yi wa mata kaciya a Majalisar Tarayyar Turai.[7]

Lafiya da Muhalli[gyara sashe | gyara masomin]

A Kwamitin Muhalli, Kiwon Lafiyar Jama'a da Tsaron Abinci ta mayar da hankali kan lamuran kiwon lafiyar jama'a, inda ta yi magana game da buƙatar tsauraran dokoki ga likitocin EU[8] da kuma tabbatar da cewa EU ba ta cika ka'idojin amfani da na'urar daukar hoto na MRI a doka.[9] Ta tsara rahoton kwamitin kan bayar da gudummawa wajen bayar da bayanai akan kwayoyin halitta da sel wanda ya bukaci a kara ba da gudummawar bargo da jini don dashen kwayoyin halitta.[10] Ita ce wacce ake tuntuɓa dangane da abubuwan da suka shafi kwamitin na "European Centre for Disease Prevention and Control".

Yannakoudakis ta jagoranci wani kamfen don tabbatar da cewa dokokin EU sun sa masu amfani da sigari saukin samun e-cig.[11]

Cyprus da 'yancin LGBT[gyara sashe | gyara masomin]

Yannakoudakis ta yi aiki don tallafawa kokarin gano mutanen da suka bace a lokacin da Turkiyya ta mamaye Cyprus da kuma rikicin kabilanci na Cyprus.[12] Ta kasance memba na "European Parliament Intergroup on LGBT Rights".[13] Ta yi fafutukar ganin an daina daukan 'yan luwadi da madigo matsayin masu laifi a Arewacin Cyprus.[14] Ta gana kuma ta samu tabbacin shugaban kasar Cyprus Dr. Derviş Eroğlu na cewa zai rattaba hannu kan soke dokar haramta luwadi a matsayin doka[15] kuma ta hanyar matsin lamba ga mahukunta a arewacin kasar ta taka rawa wajen soke dokar hana luwadi.[16][17]

Ta goyi bayan 'yancin LGBT ta hanyar ba da izini ga wani kuduri kan haƙƙin LGBT a Afirka musamman kare 'yan madigo[18] tare da yin kira ga EU da ta dakatar da taimakon da take ba Uganda bisa la'akari da dokar hana luwadi da madigo a kasar Uganda.[19]

Adawa ga manufofin EU[gyara sashe | gyara masomin]

Yannakoudakis ta yi adawa da gabatar da sabon tsarin harajin kudi na Tarayyar Turai[20][21][22] wacce ta yi imanin cewa zai yi mummunan tasiri a birnin London. Ta kuma yi kamfen don kare kamfanoni a mazabarta da dokokin EU da suka hada da Prudential plc ke yi wa barazana.[23] Ta jagoranci gangamin jam'iyyu da dama na kasa da kasa don samar da daidaiton filin wasa na masu sarrafa rake, gami da Tate &amp; Lyle na Landan inda ayyuka ke fuskantar barazana.[24][25][26][27]

Ta jagoranci yakin neman tanadi a cikin kasafin kudin EU.[28] Ta nuna damuwa game da kashe kuɗi akan ƙungiyar mawaƙa ta EU kuma ta yi kira don a rika biyan European Personnel Selection Office.[29] da Hukumomin Tarayyar Turai.[30][31] Ta soki EU da ke kashe Yuro miliyan biyu a shekara a bikin Europe Day.[32]

Yannakoudakis ta yi tsokaci da dama kan fadada EU. Ta kada kuri'ar kin amincewa da shigar Iceland cikin Tarayyar Turai[33][34] tana mai yin nuni da rigimar Icesave da ke gudana a matsayin cikas ga zamar ta memba na EU. Yannakoudakis ta yi kira ga Iceland da ta cika diyya ga duk masu ajiya a Burtaniya, musamman ma majalisun London da suka kashe rarar kudi. Ta kuma yi adawa da wani rahoton Majalisar Tarayyar Turai da ya ba da shawarar shigar Turkiyya cikin Tarayyar Turai[35] tare da nuna damuwa kan gazawar al'ummar Ankara na mutunta hakkin mata da na tsiraru, musamman Kurdawa a Turkiyya. Ta kuma yi suka ga yadda Turkiyya ta ki yin aiki da Shugabancin Cyprus ta Majalisar Tarayyar Turai a 2012.

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi aure da mijinta haifaffen garin Greek, Zacharias Yannakoudakis, a shekarar 1983. Ita ce shugabar kudi ta kamfanin da suka kafa kuma sun cigaba da gudanar da kamfanin tare har zuwa lokacin zabenta; ma'auratan suna da 'ya'ya uku. Iyalin suna zaune a Barnet .

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "European Parliament Profile". European Parliament. Retrieved 8 January 2012.
  2. Banks, Martin (17 June 2011). "New EU maternity rules 'set to be shelved'". The Parliament Magazine. Brussels. Archived from the original on 4 February 2013. Retrieved 8 January 2012.
  3. "Outcry over EU plan for more women directors". The Daily Express. London. 5 September 2012. Retrieved 5 September 2012.
  4. Morrison, Caitlin (20 December 2011). "MEP objects to ECJ ruling". Insurance Age. London. Retrieved 8 January 2012.
  5. Fleming, Jeremy (4 October 2011). "MEPs urge encouragement for female web entrepreneurs". Euractiv. Brussels. Retrieved 8 January 2012.
  6. "Protecting children from sex abuse". Conservatives in the European Parliament. Archived from the original on 9 November 2011. Retrieved 8 January 2012.
  7. Davis, Anna (3 February 2014). "Europe-wide move to end FGM barbarism". Evening Standard. London. Retrieved 9 February 2014.
  8. Banks, Martin (21 November 2011). "MEP calls for language tests for doctors". The Parliament Magazine. Brussels. Archived from the original on 11 September 2012. Retrieved 8 January 2012.
  9. Yannakoudakis, Marina (2 December 2011). "MRI ban would be 'madness' - warns MEP". PublicService Europe. Brussels. Archived from the original on 5 December 2011. Retrieved 8 January2012.
  10. "Health MEPs oppose paid donation of tissues and cells". European Parliament. Retrieved 21 July2012.
  11. Yannakoudakis, Marina (18 July 2013). "E-cigarettes key to helping smokers kick the habit". London 24. London. Archived from the original on 7 February 2014. Retrieved 9 February 2014.
  12. Banks, Martin (8 June 2011). "MEPs press for continued action to find Cyprus' disappeared". The Parliament Magazine. Brussels. Archived from the original on 21 October 2011. Retrieved 8 January2012.
  13. James Ledward, Tory MEP joins European Intergroup on LGBT rights[permanent dead link], GScene, 24 July 2012
  14. Gray, Stephen (1 February 2012). "MEPs condemn gay arrests in Northern Cyprus". The Pink News. London. Retrieved 2 February 2012.
  15. Lloyd, Peter (20 October 2011). "Conservative MEP gets pledge from Turkish Cypriot leader to repeal anti-gay law". The Pink Paper. London. Archived from the original on 20 July 2012. Retrieved 8 January2012.
  16. Roberts, Scott (27 January 2014). "Northern Cyprus votes to repeal gay sex ban". The Pink News. London. Retrieved 9 February 2014.
  17. "Northern Cyprus lifts ban on gay sex". BBC News. London. 27 January 2014. Retrieved 9 February 2014.
  18. Gray, Stephen (6 July 2012). "European Parliament condemns violence against lesbians in Africa". The Pink News. London. Retrieved 21 July 2012.
  19. Roberts, Scott (19 November 2012). "Tory MEP says EU aid must stop if Uganda passes anti-gay bill". The Pink News. London. Retrieved 4 February2013.
  20. Yannakoudakis, Marina (7 December 2011). "Tax and the City". City AM. London. Retrieved 8 January 2012.
  21. Mason, Daniel (23 January 2012). "No plot against UK, insists EU's Barnier". PublicService Europe. Brussels. Archived from the original on 19 June 2012. Retrieved 24 January 2012.
  22. Mason, Daniel (23 May 2012). "Push ahead with financial transaction tax, MEPs urge". PublicService Europe. Brussels. Archived from the original on 27 May 2012. Retrieved 7 June 2012.
  23. Nyman, Francesca (29 February 2012). "Prudential departure would be "severe blow", says Tory MEP". Insurance Insight. London. Archived from the original on 26 May 2012. Retrieved 10 March 2012.
  24. "Tate & Lyle EU sugar case backed by MEPs". The Grocer. London. 20 February 2012. Retrieved 10 March 2012.
  25. "No Sweeteners". EU Chronicle. Brussels. 10 May 2012. Retrieved 16 May 2012.
  26. Broadbent, Giles (29 May 2012). "MEPs call for reforms to help Tate & Lyle". The Wharf. London. Retrieved 7 June 2012.
  27. "MEPs lobby for 'equal treatment' for EU sugar cane refiners". Agra Europe. Brussels. 5 July 2012. Retrieved 21 July 2012.
  28. Banks, Martin (18 March 2012). "EU spends £9 million on 13 orchestras". The Daily Telegraph. London. Retrieved 16 May 2012.
  29. Banks, Martin (31 January 2013). "Commissioner leaps to defence of under-fire EU personnel office". The Parliament Magazine. Brussels. Archived from the original on 6 February 2013. Retrieved 4 February 2013.
  30. Banks, Martin (31 January 2013). "Commissioner leaps to defence of under-fire EU personnel office". The Parliament Magazine. Brussels. Archived from the original on 6 February 2013. Retrieved 4 February 2013.
  31. Banks, Martin (4 September 2012). "MEP calls for EU gender agency funding to be scrapped". The Parliament Magazine. Brussels. Archived from the original on 4 February 2013. Retrieved 5 September2012.
  32. Yannakoudakis, Marina (22 June 2012). "EU spends millions on Europe Day every year". Public service Europe. Brussels. Archived from the original on 1 February 2013. Retrieved 21 July 2012.
  33. Meade, Geoff (14 March 2012). "MEP in protest over Iceland EU membership". The Independent. London. Retrieved 15 March 2012.
  34. Nielsen, Nikolaj (15 March 2012). "Iceland considers Canadian dollar instead of euro". EUObserver. Brussels. Retrieved 15 March 2012.
  35. Banks, Martin (30 March 2012). "EU parliament told Turkey is 'not ready' for EU accession". The Parliament Magazine. Brussels. Archived from the original on 2 April 2012. Retrieved 4 April 2012.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]