Mark James (marubucin waka)
Mark James (marubucin waka) | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Francis Rodney Zambon |
Haihuwa | Houston, 29 Nuwamba, 1940 |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mutuwa | Nashville (mul) , 8 ga Yuni, 2024 |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | mai rubuta kiɗa, mai rubuta waka da singer-songwriter (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Sunan mahaifi | Mark James |
IMDb | nm1108027 |
Francis Rodney Zambon (Nuwamba 29, 1940 - Yuni 8, 2024), wanda aka sani da a wurin aiki da suna Mark James, marubuci ne ɗan Amurka ne. Ya rubuta wakoki ga mawaka irin su, B.J. Thomas, Brenda Lee da kuma Elvis Presley, wanda suka hada da Hooked on a Feeling, Always on My Mind, da kuma wakar Presley mai suna "Suspicious Minds".[1]
Kuruciya
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mark James ya kasance dan asalin Italiya da Amurka wanda aka haifa kuma ya tashi a Houston, Texas, a ranar 29 ga watan Nuwamban 1940,[2] ɗa ga wani ɗan kwangilan gine-gine kuma malamin makaranta.[3] A makaranta, ya kasance yana waka da violin kuma yana gudanar da wakokin makaranta, amma ya fada cewa bai taba sanin yadda yake kaunar waka sai da ya fara wasa da jita.[4] James ya yi abota da B.J. Thomas a lokacin duka suna yara.[5] Ya fara rubuta waka da wasannin waka a gidajen rawa a Houston, kuma canza sunan shi zuwa Mark James, bayan an fada masa cewa 'Francis Zambon' "ba wanda ya fara" bane.[6]
Fara sana'a da rubuta wakoki
[gyara sashe | gyara masomin]Da farko James ya fara rikodin wakokin shi da kan shi maimakon ya ba wasu mawakan su yi mai. Ya fara rubuta wakarsa ta farko mai "Jive Note", a cikin shekarar 1959. Ya kirkiri gungun mawaka mai suna 'Yan ukun Mark James", kuma ya saki wakoki da yawa wanda suka rubuta shi da Bobby Winder,ciki har da, Running Back and Tell Me, wanda aka saki ta gidan rikodi na Crazy Cajun Records da ke Houston, wanda karamin waka ne a shekarar 1963.[7] Sana'arsa ta waka ta dan tsaya a lokacin da aka saki sunanshi acikin sojojin Amurka don yin aiki a Vietnam, a cikin Rukunin Sojojin Yaki na Farko.
Bayan an sallame shi, ya koma garin Memphis, kuma ya yi aiki a matsayin cikakken ma'aikaci ga kamfanin wallafawa na furodusan garin Memphis, Chips Moman.[5] A cikin shekarun 1968 da 1969 Moman ya shirya nau'in wasan Thomas kamar "The Eyes of a New York Woman", "Hooked on a Feeling", da kuma "It's Only Love", wanda duka sun yi nasara.[8] Wakarsa mai suna "Hooked on a Feeling" wanda ya rubutawa budurwarsa ta kwaleji Karen Taylor, da kuma "Suspicious Minds" sun kasance na farko daga cikin wakokin sa guda goma na musamman.[9]
James ya saki nau'in bugun wakarsa mai suna "Suspicious Minds", wanda kuma Moman ne ya shirya, a gidan rikodi na Scepter Records a cikin shekara ta 1968. Elvis Presley a yayin neman wakar da zai sabunta sana'arsa ya nemi Moman da ya kunna masa wakar "Suspicious Minds", kuma yayi rukodin nau'inta a shekara ta 1969 da shirin kusan iri daya. Wakar ta zamo cikin manyan wakoki, kuma shigar da ita a cikin jerin wakoki 500 wanda sukafi daukaka na kowanne lokaci - Rolling Stone's 500 Greatest Songs of All Time kuma itace na 91.
1969–1977: Cigaban nasarori
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekara ta 1972, James ya sanya hannu tare da kamfanin Screen Gems-Columbia Music. A cikin shekara ta 1973 kuwa, wakarsa mai suna "Sunday Sunrise" wani mawakin asalin Amurka mai suna Brenda Lee ne yayi rikodin wakar. Bugun na Lee ta shahara sosai kuma ta zamo daga cikin wakoki goma na musamman a Amurka a cikin shekarar 1975. Mawakiyar kasar Kanada mai suna Anne Murray ita ta hau wakar "Sunday Sunrise". Elvis Presley ya yi rikodin wakokin James da dama, ciki har da "Raised on Rock", "It's Only Love" da kuma "Moody Blue", wanda suka zamo wakokin karshe na sutudiyo ga Presley. Daukakar James na musamman ta zo ne tare da wakarsa mai suna "Always on My Mind", wanda ya rubuta tare da Johnny Christopher da kuma Wayne Carson. A cikin shekara ta 1973, gungun mawakan jazz mai suna Blood, Sweat & Tears sun saki wakar James mai suna "Roller Coaster" a matsayin waka daga cikin albam din su mai suna "No Sweat". David Cassidy ya buga wannan waka a cikin wannan shekara a matsayin albam na karshe na Partridge Family mai suna Bulletin Board, wanda take dauke da wasu wakokin guda biyu na James masu suna "Where Do We Go From Here" da kuma "Alone Too Long", wanda ya rubuta tare da Cynthia Weil.
Daga 1978: Nasarar lashe Grammy, wakokin "Always on My Mind", da 'Yan Ukun Mark James.
[gyara sashe | gyara masomin]Gungun 'Yan Ukun Mark James sun saki waka mai suna She's Gone Away a cikin shekarar 1960, tare da mambobin mawakan kungiyar Joey Longoria da Bobby Winder wanda suka rubuta wakar tare da Mark James.
Bayan shekaru goma kuma, an saki wakar "Always on My Mind", Willie Nelson ya hau wakan kuma ya mayar da ita shahararriyar waka. James ya lashe Kyautar Grammy ta Wakar Shekara , don bugun wakarsa da Nelson ya hau. A cikin shekara ta 1987, gungun mawakan UK mai suna Pet Shop Boys sun saki nau'in wakar "Always on My Mind", wacce ta zamo ta 1 a UK sannan kuma ta 4 a US. A ranar 11 ga watan Oktoban 2015, James ya shiga Zauren Shahararrun Marubatan Wakoki na Nashville.
Rayuwa da mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]James ya auri matarsa ta farko Shirley Yates, a Houston, Texas. Suna da 'ya mace. Ya auri matarsa ta biyu Karen Taylor, a 1971. Tana da 'ya mace daga aurenta na farko. Mark James ya mutu a gidan shi a Nashville, Tennessee, a ranar 8 Yuni, 2024, a lokacin yana da shekaru 83.[10][11][12]
Lambobin yabo
[gyara sashe | gyara masomin]Kyautar Grammy
[gyara sashe | gyara masomin]1983 | "Always on My Mind" | Kyautar Grammy Award don wakar shekara | ya lashe |
1983 | "Always on My Mind" | Kyautar Grammy don wakar kasa ta musamman | ya lashe |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Jones, Roben (February 1, 2010). Memphis Boys: the Story of American Studios. Univ. Press of Mississippi. p. 19. ISBN 978-1-60473-401-0. Retrieved November 22, 2010.
- ↑ Edwards, Joe (September 22, 1985). "Nashville Sound: Encouraging Word Spurred Career". The Victoria Advocate. Retrieved September 7, 2012.
- ↑ Mark James obituary, The Times Register, 14 June 2024
- ↑ Mark James obituary, The Times Register, 14 June 2024
- ↑ 5.0 5.1 Klein, George; Crisafulli, Chuck (January 5, 2010). Elvis: My Best Man: Radio Days, Rock 'n' Roll Nights, and My Lifelong Friendship with Elvis Presley. Crown. p. 194. ISBN 978-0-307-45274-0. Retrieved November 22, 2010.
- ↑ Mark James obituary, The Times Register, 14 June 2024
- ↑ Mark James obituary, The Times Register, 14 June 2024
- ↑ Collins, Ace (April 1, 2005). Untold Gold: The Stories Behind Elvis's #1 Hits. Chicago Review Press. p. 213. ISBN 978-1-55652-565-0. Retrieved November 22, 2010.
- ↑ Mark James obituary, The Times Register, 14 June 2024
- ↑ "Mark James Obituary". Harpeth Hills Memory Gardens-Funeral Home & Cremation Center. Retrieved June 11, 2024.
- ↑ Brodsky, Greg (June 11, 2024). "Mark James, Songwriter of 'Suspicious Minds' and Other Hits, Dies". Bestclassicbands.com (in Turanci). Archived from the original on June 11, 2024. Retrieved June 11, 2024.
- ↑ Dansby, Andrew (2024-06-11). "Mark James, Houston songwriter known for Elvis Presley hit 'Suspicious Minds,' has died". Houston Chronicle. Retrieved 2024-08-26.